Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

N-HYPPADEC Ta Raba Kayyakin Aiki Ga Dalibai Sama Da 5000 Da Suka Koyi Sana'o'in Hannu

Daga Awwal Umar Kontagora N-HYPPADEC ta raba kayyakin aiki ga dalibai sama da dubu biyar da suka koyi sana'o'in hannu daban daban sa...



Daga Awwal Umar Kontagora

N-HYPPADEC ta raba kayyakin aiki ga dalibai sama da dubu biyar da suka koyi sana'o'in hannu daban daban sama da goma sha takwas.

Tunda farko a bayanin babban daraktan hukumar, Alhaji Abubakar Sadiq Yelwa ( Katukan Yauri) yace an kaddamar da shirin ne a shekarar 2022, har zuwa 2023 inda aka horar da matasa sama da dubu 5000, a karkashin shirin Youth Transformation Program.

Sadiq Yelwa, ya cigaba da cewar shirin ya shafi jahohi shida da ke karkashin kulawar hukumar, yayin da jihar Neja ta samu gurbi 1500 cikin 5000 da suka shiga shirin.

Katukan Yauri, ya jawo hankalin matasan da su tabbatar sun yi anfani da kayyakin da aka ba su, dan cigaba da sana'o'in da suka koya dan samun dogaro da kan su, ya kara da cewar hukumar N-HYPPADEC ta kirkiro wannan shirin duba da irin da dubban matasa ke ciki na raahin aiki, wanda muka cewar kundugurin tarayya shi ne kirkiro hanyoyin da dubban matasa zasu samu madogarar rayuwa.

Dan haka, ya jawo hankalin wadanda suka samu wannan damar,da su tabbatar ba su karkatar shi a hanyar da bai dace ba. Domin duk wani abinda suke bukata dan gudanar da sana'o'in da suka koya kuma suna bukatar cin gajiyar shi mun ba su, bayan nan mun masu rajista da hukumar yiwa kamfanoni da sana'o'i rajista dan tabbatar sun tsaya da kafarsu, fatar bayan su ya zama al'umma sun anfana da wannan sana'ar ta hanyar koyar da wasu.

Da yake bayani, kwamishinan matasa, Hon. Yahaya Ibrahim Gulbin-Boka, ya yabawa wannan hukumar bisa damar da ta baiwa matasan Neja, wanda yace matasan jiha zasu anfana da kudurorin gwamnatin tarayya na samar da ayyuka ga al'ummar kasar na samun damar dogaro da kai wanda yayi daidai da kudurin gwamnatin jiha, bisa jagorancin babban manomi, Hon. Umaru Mohammed Bago wanda ya kuduri aniyar samar da gurabun ayyuka miliyoyi ga matasan jihar nan.

Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, wanda ya samu wakilcin Mista Simon Tungu, yace gwamnatin tarayya ta karfafa guiwar wannan hukumar dan inganta rayuwar al'ummomin da ke zaune a yankunan da ke samar da wutan lantarki na kasa, musamman dan inganta rayuwa da samar da madogara ga al'ummar kasar nan.

A cewar sakataren, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a shirye take wajen ganin ta tsamo al'ummomin kasar nan daga talauci, rashin aikin yi da tsadar rayuwa musamman duba da ganin irin kudurce kudurcen ta na inganta tattalin arzikin kasar nan.

Sanata Sani Musa, shugaban kwamitin kudi na majalisar dattijai, yace dukkanin wani kudin da majalisa za ta amince da fitarwa da kashewa ga gwamnatin tarayya, majalisar za ta tabbatar ba yi jan kafa wajen inganta rayuwar al'ummar kasar nan ba.

Mai martaba Etsu Nupe, shugaban majalisar sarakunan jihar Neja, Dr. Yahaya Abubakar, ya jawo hankalin wadanda suka samu wannan kyauta, da su tabbatar sun yi anfani da shi wajen cigaban yankunan su, ta hanyar kirkiro hanyoyin da zasu anfanar da wadanda ba su samu irin wannan damar ba.

Etsu Nupe, yace rike sana'ar hannu zai taimakawa matasa wajen samun aikin yi, da kuma dogaro da kan su wajen yaki da rashin aikin yi, da kuma ba su dama wajen bunkasa rayuwarsu.

Babban manomin jiha, gwamna Neja, Hon. Umaru Mohammed Bago, ya yabawa hukumar N-HYPPADEC, wajen baiwa matasan jihar irin wannan damar, ya bada tabbacin gwamnatinsa a shirye take wajen cigaba da hada kai da duk wata hukuma da za ta bada gudunmawa ga al'ummar jihar nan.

Gwamnan, yace gwamnatinsa tana kudurin samar da miliyoyin gurabun ayyuka ga al'ummar jihar nan, musamman bangaren noma, kasuwanci da sana'o'in hannu. Ya hori wadanda suka ci wannan gajiyar da su guji karkatar da abubuwan da aka ba su a hanyoyin da ba su dace ba.

Sun jure na tsawon shekaru biyu, dan ganin wannan muhimmiyar ranar, da haka su tabbatar sun taka muhimmiyar rawa kafin nan da shekara daya dan bunkasa sana'o'in su, da kuma tabbatar sun koyar da wasu dan samun cigaban yankunan su da kuma kawo karshen fargabar rashin ayyuka yi ga matasa.

Matasa sama da dubu biyar ne aka horar a sana'o'in hannu daban daban guda goma sha takwas a jahohi shida da ke karkashin kulawa hukumar na yankunan da ke samar da wutan lantarki a kasar nan, yayi da matasa dubu daya da dari biyar da goma sha bakwai da suka fito daga yankunan kananan hukumomi goma sha bakwai cikin ashirin da biyar da ke jihar Neja suka ci gajiyar shirin, karkarin shirin inganta rayuwar matasa na hukumar N-HYPPADEC ta kasa. 

No comments