Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ambaliya Ta Mamaye Sassan Birnin Barcelona

  Barcelona ya zama birni na baya-bayan nan da aka fuskanci ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a Sifaniya, inda ruwa ya kai ga shiga wasu sass...

 


Barcelona ya zama birni na baya-bayan nan da aka fuskanci ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a Sifaniya, inda ruwa ya kai ga shiga wasu sassan filin jirgin birnin.

Wani bidiyo ya nuna matafiya suna yawo a sassan da ambaliyar ruwa ta mamaye suna jan akwatunansu.

Lamarin ya shafi tashi da saukar jirage da dama, yayin da ambliyar ta mamaye har da manyan titunan da ke kusa.

Hukumar kula da yanayi ta ƙasar ta sanya wasu sassan yankin Cataloniya cikin shirin ko-ta-kwana domin fuskantar mamakon ruwan sama.

Kafofin yada labarai na ƙasar sun nuna hotunan wasu motoci da ke nutsewa a kan wata babbar hanya.

No comments