Daga Hussaini Yero Shugaban ma’aikatan jihar Zamfara Ahmad Liman wanda kuma shi ne shugaban kwamitin tantancewa da aiwatar da sabon mafi ka...
Daga Hussaini Yero
Shugaban ma’aikatan jihar Zamfara Ahmad Liman wanda kuma shi ne shugaban kwamitin tantancewa da aiwatar da sabon mafi karancin albashi na dubu saba'in ya bayyana cewa kwamitinsa na tantance dukkan ma’aikatan jihar ya gano ma’aikatan bogi da dama a cikin jadawalin albashin Zamfara da suka hada da likitocin bogi 20 a wani asibiti a jihar.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan shirin gwamnatin Zamfara na aiwatar da mafi karancin albashi na 70,000.
Gwamnati ta kafa kwamitoci da za su tantance hakikanin adadin ma’aikatan jihar da kuma bayar da shawarwari akan sabon tsarin albashin.
Ahmad Liman ya jaddada kudirin gwamnatin jihar Zamfara na aiwatar da cikakken tsarin mafi karancin albashi da zarar kwamitin ya mika rahotonsa a karshen wata.
Ya ci gaba da cewa kwamitin na aiki tukuru don ganin an yi cikakken aiki da nufin tsaftace alkaluman lissafin albashin jihar domin aiwatar da albashi yadda ya kamata.
Kuma Babban kalubalen da muke fuskanta shine ana yi wa wasu ma'aikatan aringizon albashi wasu kuma suna amsar albashi kashi biyu a cikin jihar.
No comments