Daga Hassan Ibrahim A satin da ya gabata ne Jaridar Taskira ta karrama Sarkin Samarin Anchau Alhaji Hussaini Musa bisa irin gu...
Daga Hassan Ibrahim
A satin da ya gabata ne Jaridar Taskira ta karrama Sarkin Samarin Anchau Alhaji Hussaini Musa bisa irin gudummuwar da yake bayarwa na ci gaban matasa a yankin wanda ya gudana a Sakatariyar ƙungiyar Malamai (NUT) dake Tukur Tukur, Zariya.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kamfanin jaridar Taskira Alhaji Yusuf Abdullahi wanda ya sami wakilcin Editan jaridar Mustapha Kajuru ya ce sun zaɓo Sarkin Samarin ne bisa binciken sirri da suka gudanar a kansa, na taimakawa wajen ci gaban matasa, wanda yana da muhimmanci a ƙara karfafa masa guiwa domin ya ƙara jajircewa don ci gaban matasa a yankin da ma jihar Kaduna baki ɗaya.
Shi ma da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan amsar lambar yabon, Sarkin Samarin Anchau Alhaji Hussaini Musa ya yi godiya ga Allah SWT na ganin wannan rana mai cike da tarihi a rayuwarsa.
Alhaji Hussaini ya kuma miƙa cikakken godiyar sa ga shuwagabannin wannan jarida bisa wannan karramawar da suka yi masa.
Ya na mai cewa ba zai yi ƙasa a guiwa ba wajen ci gaba da ƙara jajircewa kan abin da ya shafi ci gaban matasa kasancewar su ne shuwagabannin gobe wanda ya na da muhimmanci su bai wa fannin ilimi muhimmanci domin ci gaba su a cikin zamantakewa na rayuwa.
A cewarsa ilimi shi ne ginshiƙi kuma fitila dake haskaka wa a rayuwar ɗan Adam.
Sarkin Samarin ya kuma yi addu'ar samun dawwamammen zaman lafiya ƙaruwar arziki da cigaba mai ɗorewa a masarautar Zazzau jihar Kaduna da ma Nijeriya baki daya.
No comments