Daga Awwal Umar Kontagora Ma'aikatar kula da jin dadin manoma da makiyaya ta shirya taron masu ruwa da tsaki dan wayar da ...
Daga Awwal Umar Kontagora
Ma'aikatar kula da jin dadin manoma da makiyaya ta shirya taron masu ruwa da tsaki dan wayar da su da neman hadin kan al'ummar fulani kan shirin gwamnatin jiha na shirin fara kidayar makiyaya a jihar wanda za a fara shi nan bada jimawa ba.
Da yake jawabi a wajen taron, kwamishinan ma'aikatar, Hon. Umar Ahmed Rebe ya bayyana cewar babban manomin jiha, gwamna Umaru Mohammed Bago na da kudurin samun cikakken kudin bayanai na al'ummar makiyaya a jihar Neja.
A cewarsa sakamakon kudurin gwamnatin jiha na kawo shirye shiryen inganta rayuwar al'umma wanda ana bukatar fulani makiyaya su ci moriyarsa ya zama wajibi a samar da sahihin kudin da za a samu adadinsu da wuraren zaman su domin gwamnati na bukatar tantance makiyaya da ke zaune a jiha da baki masu shigowa ta yadda za a iya sanin hakikanin wadanda zasu iya cin moriyar shirye shiryen gwamnati.
Taron wanda ya samu halartar sarakunan fulani da ardo-ardo ta yadda za a samu saukin isar da sakwanni ga fulanin da ke zaune a cikin karkaru.
Daga cikin ma'aikatun da suka sha alwashin bada gudunmawa dan ganin shirin ya tabbata sun hada da ma'aikatar kula da kananan hukumomin jihar, sai Ma'aikatar kula da tsare tsare, da Ma'aikatar kula da adana bayanan gwamnati a yanar gizo, da dukkanin bangarorin jami'an tsaro na jiha.
Haka kuma kungiyoyin fulani na Miyetti Allah Cattle Breaders da Miyetti Allah Kautal Hore, Gan-Allah Fulani Cultural Association sun halarci zaman dan samun saukin isar da sakon ma'aikatar ga mambobinsu na jiha.
Shirin wanda kwamishinan ya bayyana cewar zai kasance mataki biyu, inda za a fara da kananan hukumomi goma sha hudu a matakin farko sannan sauran kananan hukumomi sha daya su biyo baya a mataki na biyu.
Hon. Umar Ahmed Rebe, ya hori sarakunan da ardo-ardo da su horar da al'ummomin makiyaya da su baiwa gwamnatin jiha hadin kai dan ganin an samu nasarar wannan aikin.
Tunda farko dai, gwamnatin jihar Neja ta kirkiri wannan ma'aikatar ne dan ganin an samar da kafar da gwamnati za ta samu saukin sanin halin da makiyaya da manoma ke ciki da samun damar bunkasa bangaren noma da kiwo a jihar Neja, wannan ma'aikatar itace irinta ta farko da gwamnatin jiha ta kirkira wanda aka bata cikakkiyar damar gudanar da ayyuka dan inganta rayuwar al'umma.
No comments