Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE
Thursday, June 19

Pages

Labarai:

Shirin Gwamnatin Neja Na Ƙidayar Makiyaya: Manufa Da Ƙudurin Da Ake Son Cin Ma

Daga Awwal Umar Kontagora  A karon farko gwamnatin jihar Neja, bisa jagorancin babban manomin jiha, Gwamna Umaru Mohammed Bago, ta zama gw...



Daga Awwal Umar Kontagora 

A karon farko gwamnatin jihar Neja, bisa jagorancin babban manomin jiha, Gwamna Umaru Mohammed Bago, ta zama gwamnati na farko a arewacin Nijeriya da ta kirkiro ma'aikatar kula da jin dadin manoma da makiyaya, ma'aikatar wadda aka kirkiro ta ƙarƙashin ma'aikatar kula da harkar noma.

Ma'aikatar kula da jin dadin manoma da makiyayan za ta mayar da hankalin ta wajen samar da fahimtar juna tsakanin manoma da makiyaya, ta hanyar farfado da zaman lafiya a tsakaninsu, samar da kyakkyawar fahimta tsakanin yan uwan biyu, kyautata zamantakewa, alaka ta gaskiya da gujewa shiga hakkin juna. 

Haka ma'aikatar ana kyautata zaton za ta bullo da shirye shiryen inganta rayuwar manoma da makiyaya musamman wajen samar masu da kayan more rayuwa da ya shafi kulawa da ilimin yayan makiyaya, samar da ruwan sha mai tsafta, bunkasa kananan kasuwanci dan mata da matasa a yankunan karkaru da rugage. 

Hon. Umar Ahmed Sanda Rebe, shi ne mutum na farko da yake jagorantar wannan sabuwar Ma'aikatar a matsayin kwamishina. 

Ma'aikatar tana da tsare tsaren aiki kamar kowace ma'aikata ta gwamnati wadda ke aiki akan doka. Hakan ya nuna cewar babban manomin jiha, gwamna Umaru Mohammed Bago yayi tsayin daka wajen ganin majalisar jiha tayi abinda ya dace na doka danganin wannan ma'aikatar ta zauna da gindinta.
 
Ganin irin tsare tsaren da gwamnatin jiha ke son aiwatarwa dan anfanin al'ummar makiyaya da manoma, gwamnatin jiha ta ga akwai bukatar samar da kyakkyawar fahimta tsakanin manoma da makiyaya, tare da baiwa jami'an tsaro damar shiga dan ganin an samu fahimta tsakanin manoma da makiyaya tare da janyo masu ruwa da tsaki na kowani bangare, sarakunan gargajiya, kungiyoyi, matasa maza da matasa dan cin anfanin shirye shiryen gwamnatin. 

Wani yunkurin cigaba da gwamnatin Bago ta samarwa ma'aikatar shi ne samar da sahihin bayanai game da makiyaya da ke jihar, adadin yawan su lungu da sako, adadin dabbobin da suke kiwo da yawan matsugunnai ko rugaggen da suke zama. 

Wannan wata dubara ce da gwamnatin jiha ke yi musamman dan saukakawa kan ta yadda za ta gabatar da kasafin kudin jihar ga majalisar dokoki domin ganin an cigaba da tafiyar da lamurra ba tare da kauce ka'idar doka ba. 

Cikin shirin gwamnatin jiha akwai yunkurin inganta kasuwar nama, madara da man shanu wanda a tsarin gwamnatin da ta baiwa ma'aikatar shi hanyoyin da za a bi wajen rage dawainiyar yawon kiwace kiwace ga yayan makiyaya dan ba su damar tsayawa dan neman ilimi musamman kamar yadda kwamitin kula da ilmantar da yayan mazauna karkaru na majalisar dunkin duniya. 

Tsarin ilimin kimiyya da ya zamana duniya ta amince da shi, ba zai samu karbuwa ba, dole sai gwamnati ta bada kulawa ta musamman. 

Bayan nan akwai barazanar tsaro wanda batagari kan yi anfani da damar rashin ilimi ga al'ummomin karkara wajen kwadaitar da matasa suna fadawa saboda rashin sanin illarshi ga rayuwarsu. 

Samar da kididdiga da cikakken kundin bayanai zai bada damar sanin bakin makiyayan da ke ratsowa suna yada mikayagun akidu ko su aikata barna su gudu ba tare da sanin inda suka fito ba, su gudu su asalin makiyayan mazauna cikin damuwa. 

Dan haka akwai bukatar masu ruwa da tsaki musamman sarakunan gargajiya, ardo-ardo da kungiyoyin fulani makiyaya, irinsu Miyetti Allah Kautal Hore, Miyetti Allah Cattle Breaders da Gan-Allah Fulani Cultural Association da su tashi tsaye wajen fadakar da al'ummomin makiyaya sanin muhimmancin wannan kidayar, domin baiwa gwamnatin hadin kai da goyon baya. 

Arziki baya yalwanta muddin ba zaman lafiya, ba a samun cigaba muddin ba hadin kai, al'umma ba ta bunkasa muddin an tsere mata a fagen ilimi. Gwamnati! ba ta sanin matsalolin al'umma muddin ba a kasance ta ba, wajibi ne kowani dan kasa na gari ya zauna lafiya da abokin zamansa, wadannan ba sa samuwa sai an kawar da kabilanci, son rai tare da kishin kasa.



No comments