Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar shirya bukin mauludin Manzon Allah da almajiran Madarasatul El-kareem da ke gudanar da harkokinta...
Daga Awwal Umar Kontagora
An bayyana cewar shirya bukin mauludin Manzon Allah da almajiran Madarasatul El-kareem da ke gudanar da harkokinta na yada addinin musulunci da ke unguwar FM a gundumar Maitumbi da ke cikin garin Minna, tana shirya shi ne bisa soyayyar Manzon Allah da ta ginu akan shi. Shugaban kungiyar Mahaddata Al-kur'ani mai tsalki da malaman tsangaya ta kasa reshen jihar Neja, Imam Hussaini Abubakar Shakwata ne ya bayyana hakan a yammacin asabar din makon nan mai karewa lokacin gudanar mauludin Manzon Allah da almajiran Madarasatul El-kareem ta shirya na wannan shekarar.
Imam Hussaini, ya cigaba da cewar son Manzon Allah itace asalin kimiyya ta fasaha, muddin babu soyayyar Manzon Allah a zuciyar mutum tabbas yayi hasarar kimiyyarsa.
Asalin kimiyyar nan itace asalin dabiu da kyawawar ma'amalar Manzon Allah da jama'a, yace wani daga cikin magabata da aka tambaye shi irin soyayyar sa da manzon Allah, sai yace tun kafin halitta aka halarci soyayyar sa da Manzon Allah, dan haka ba zai iya kwatanta irin soyayyar Manzon Allah da ke cikin ruhinsa ba, babban abinda soyayyar nan ke koyarwa, shi riko kyawawan halayen Manzon Allah, idan ka samu soyayyar Manzon Allah, ka tsayu akan dabi'unsa, da koyarwa sa ka gama samun tsira wadda za ta kai Ka ga tudun natsira.
Da ya juya kan nasarar da ya samu bisa jagorantar wannan kungiyar ta Huffazu Qur'an and Scholars Association of Nigeria reshen jihar Neja. Yace babban nasarar mu itace hadin kai, nasara ta biyu ba a taba samun gwamnati da ta tafi mu ba, kamar wannan gwamnatin ta babban manomin jiha, gwamna Umaru Mohammed Bago, domin ya ba mu mukaman kudinetoci guda uku, Neja ta Arewa, Neja ta tsakiya da kuma Neja ta kudu, bayan nan muna da mukaman masu baiwa gwamna shawara, wannan babban nasara da muka samu.
Na uku akwai kwamitin da gwamnatin jiha ta kafa bisa jagorancin Alhaji Shu'aibu Gwada mun zauna mun tattauna kuma da yardar Allah idan gwamnati ta amince da rahoton kwamitin shi ma nasara ce babba.
Da ya juya kan rikicin kungiyar Markaz Ulumul-Qur'an ta kasa da ke ikirarin shugabanni guda biyu a matakin kasa kuwa, yace mu kungiyar The Huffazul Qur'an and Scholars Association of Nigeria kungiya ce mai zaman kan ta, amma muna da kyakkyawar fahimta da Markaz, saboda haka maganar shugabancin bangarori biyu har yanzu ba mu mika mubayi'armu ga kowa ba, akwai matakai da hanyoyin da muke bi dan a samu maslaha da yardar Allah nan ba da jimawa ba zamu warware wannan matsalar domin rarrabuwan kan malaman addini da ke kokarin hada kan al'umma iftila'i ne, da yardar za a daidaita tsakani.
Imam Hussaini, ya jawo hankalin al'umma wajen koyi da halayen Manzon Allah, sannan mu kara kaimi wajen kulawa da tarbiyar yara da karantar da su Al-kur'anin mai tsalki.
No comments