Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dole Mu Rungumi Fasahar Zamani Wajen Yaki Da Matsalolinmu -Shettima

Mataimakin shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, a yayin da yake jaddada bukatar amfani da dabarun fasahar zamani wajen yaki da ta'addanci...



Mataimakin shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, a yayin da yake jaddada bukatar amfani da dabarun fasahar zamani wajen yaki da ta'addanci, da manyan laifukan da ake aikatawa ta yanar gizo, da ma sauran kalubalen tsaron kan iyaka a Najeriya da Afirka baki daya. 

Shettima ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin gudanarwa na sashen sarrafa bayanan sirri na 17 karkashin Cibiyar Nazarin Tsaro ta kasa (NISS) a fadar   

Masu ziyarar suka ce Kwas ɗin ya mayar da hankali kan " Samar da hanyoyin Ƙarfafa Tattalin Arziki a Afirka tare da dakile Kalubalen da nahiyar ke fuskanta a fannin dasaha.

Shettima ya bayyana yuwuwar amfani da kirkirarriyar basirar (AI) wajen magance batutuwan da suka shafi noma, kiwon lafiya, hada-hadar kudi, da tsaro. 

Mataimakin ya kuma karfafa gwiwar matasan Afirka da su shiga a dama da su a fannin basirar AI don samar da ci gaban nahiyar 

Mataimakin shugaban kasar ya kuma ambaci kamfanonin Najeriya masu nasara, irin su Moniepoint, Interswitch, Flutterwave, da OPay, a matsayin misalan karfafa gwiwar 'yan kasar a fannin kirkire-kirkire inda ya kalubalanci shugabanni da kara azama wajen karfafa gwiwar gaba yan kasa da himmatuwa wajen tunkarar kalubalen da Najeriya da nahiyar Afirka ke fuskanta.

No comments