Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta yi watsi da kudurin dokar sake fasalin haraji, tare da gargadin cewa yana barazana ga hadin kan kasa. Kung...
Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta yi watsi da kudurin dokar sake fasalin haraji, tare da gargadin cewa yana barazana ga hadin kan kasa.
Kungiyar ta soki yadda aka aiwatar da ita, inda ta yi zargin cewa an mayar da masu ruwa da tsaki ciki har da membobin majalisar tattalin arzikin kasa a gefe a yayin gudanar da aikin.
Shugaban kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ne ya bayyana hakan bayan taron kwamitin amintattu karo na biyu na shekara-shekara, a Abuja.
No comments