Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Farfesa Gwarzo Ya Bai Wa Foliteknik Ta Gwamnatin Tarayya Ta Kabo Tallafin Mota Ƙirar Bas Mai Kujeru 60

  Shugaban gamayyar jami’o’in MAAUN Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bayar da tallafin motar alfarma mai cin kujeru 60 ga Foliteknik ta Gwa...

 


Shugaban gamayyar jami’o’in MAAUN Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bayar da tallafin motar alfarma mai cin kujeru 60 ga Foliteknik ta Gwamnatin Tarayya dake Kabo a jihar Kano.

Ya ce motocin za su saukaka zirga-zirgar ma’aikata da daliban makarantar ta gwamnatin tarayya.

Farfesan ya sanar da bayar da tallafin ne a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da ya kai ziyarar nuna goyon baya ga shugaban makarantar, Farfesa Magaji Sanusi.

Farfesa Magaji ya rike mukamin shugaban riko na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya dake Kano.

Kafin wannan rana, a wajen taron bikin yaye dalibai karo na tara na Jami’ar Tarayya da ke Dutsimma a Jihar Katsina, Farfesa Gwarzo ya kuma bai wa jami’ar kyautar motar bas mai dauke da kujeru 60 na alfarma domin saukaka wa dalibai da ma’aikata wajen zirga-zirga.

A baya dai Farfesa Gwarzo, ya bayar da wata motar bas ta alfarma ga Jami’ar Al-Istiqama da ke Sumaila a Jihar Kano.

Farfesa Gwarzo, hamshakin dan kasuwa kuma mai kishin ci gaban ilimi mai taimakon al’umma, shi ne wanda ya kafa Jami’o’in Maryam Abacha da ke Maradi, a Jamhuriyar Nijar; da Jami’o’in Maryam Abacha da ke Kano, Nijeriya; Franco British International University, Kaduna; da kuma Jami'ar Kanada ta Nijeriya a Abuja.

A garin Kabo, wanda ya assasa jami’o’in na MAAUN ya taya Farfesa Magaji murnar nadin da aka yi masa a matsayin farkon shugaban wannan babbar Foliteknik.

“Wannan rana ce ta musamman a gare mu, domin an nada daya daga cikin mu a matsayin shugaban wannan cibiya ta ilimi. Ina taya ma’aikata murna saboda mutum ne mai basira da zai bunkasa wannan cibiyar ilimin,” inji shi.

Farfesa Gwarzo ya bukaci ma’aikatan makarantar da su bai wa Farfesa Magaji goyon baya da hadin kai da ake bukata domin ba shi damar kawo ci gaban da ake bukata a sabuwar makarantar ta yadda za ta yi gogayya da sauran takwarorinta a fadin kasar nan.

No comments