Daga Awwal Umar Kontagora Mataimakin gwamnan Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida ya ƙaryata labarin da ake yadawa na kwace wani kauye da ...
Daga Awwal Umar Kontagora
Mataimakin gwamnan Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida ya ƙaryata labarin da ake yadawa na kwace wani kauye da ake cewar yan bindiga sun yi, a cewarsa labarin ba shi da tushe balle makama.
Sanata Umar ya bayyana labarin da cewar ƙirƙirar ƙarya ce kawai irin ta masu rubutu a yanar gizo.
Mataimakin gwamnan ya ƙara da cewar gwamnatin jiha da haɗin guiwar jami'an tsaron jihar suna bakin kokarin wajen tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar da kuma bayar da kariya ga dukkanin ƙauyukan jihar daga dukkanin wani hari na ɓata gari ko ƴan ta'adda.
Mataimakin gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake wata zantawa ta musamman da manema labarai a garin Birnin Kebbi fadar gwamnatin jihar.
Mataimakin gwamnan ya tabbatar da labarin da ya faru a garin Mera wanda Yan ta'addan Lakurawa suka kaima hari wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane goma sha bakwai inda suma al'ummar garin Mera suka yiwa yan ta'addan raunuka a bata kashin da aka yi a lokacin harin.
Bayan samun labarin wannan harin ne jami'an gwamnatin jiha da ƴan majalisu suka kai ziyara a ƙauyen kuma suka bayar da tallafi daban-daban tare da tabbatar jami'an tsaron jihar sun ɗauki dukkanin matakan da suka dace na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Daga cikin manyan jami'an gwamnati da suka baiwa al'ummar garin tallafi sun haɗa da:
1. Gwamnan Jihar Kebbi Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu: ₦50m
2. Tsohon Gwamnan Jahar Kebbi kuma ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin Najeriya Sanata Abubakar Atiku Bagudu CON: ₦30m
3. Ƴan majalisun tarayya: ₦10m
4. Ƙaramin Ministan harkokin Jinƙai da yaƙi da fatara Honorabul Dakta Yusuf Tanko Sununu: ₦2.5m
Mataimakin gwamnan ya tabbatar da cewar gwamnatin jihar Kebbi ta aikawa rundunar sojoji ta ƙasa da wakilai na musamman domin sanar da su halin da jihar take ciki da kuma neman cikakken goyon bayansu wajen magance matsalolin tsaro a jihar.
Wannan tawagar da gwamnatin Kebbi ta aikawa rundunar sojojin Njjeriya tana karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar kuma Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya Sanata Abubakar Atiku Bagudu CON.
Haka kuma wannan tawagar ta ƙunshi Sanata Bala Ibn Na'Allah, da sakataren tsare-tsaren jami'yar APC na ƙasa, Alhaji Suleiman Argungu, tsohon kwamishinan Shari'a na jihar Kebbi, Barista Nasiru Junju da dai sauransu.
Mataimakin gwamnan ya baiwa al'ummar jihar tabbacin cewar gwamnatin jiha tana ɗaukar dukkanin matakan da suka dace wajen baiwa dukiyoyi da rayukan al'ummar jihar kariya inda yayi kira ga al'ummar jihar da su baiwa jami'an tsaron jihar goyon bayan da ya dace domin cin nasarar samar da ingantaccen tsaro a fadin jihar.
No comments