Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Magoya Bayan Ƙungiyoyin Firimiya Huɗu Za Su Yi Zanga-Zanga

  Magoya bayan Everton da Liverpool da Manchester City da United sun haɗa ƙarfi wuri daya domin gudanar da zanga-zanga a wannan makon kan ta...

 

Magoya bayan Everton da Liverpool da Manchester City da United sun haɗa ƙarfi wuri daya domin gudanar da zanga-zanga a wannan makon kan tashin farashin tikitin shiga kallon kwallo.

Sun samu goyon bayan ƙungiyar magoya bayan kwallon ƙafa ta Ingila kan hakan, Magoya bayan United da na Everton sun yi shirin ɗaga kwalaye ɗauke da 'Ku dakata da tatsar magoya bayanku' gabanin wasan da za su yi a Old Trafford a ranar Lahadi.

A Anfield da Liverpool za ta karbi baƙungin Manchester City, magoya bayan ƙungiyoyin biyu za su ɗaga kwalaye kamar na takwarorinsu Everton da Man Utd.

Ana zargin Manchester United da tatsar kudi daga magoya bayanta bayan hukuncin da suka yanke a tsakiyar kaka na ɗaga farashin tikitin wasanni zuwa fan 66 kowanne wasa, ba tare da duba yara ko kuma masu karɓar fansho.

Manchester United ba ta ƙoƙarin a zo a gani a kakar bana, wani abu da magoya bayanta da na Everton suka ce ba sa jin dadi, amma duk da haka ana neman ƙara msu farashin tikiti.

Liverpool ta ƙara farashin tikiti a wannan kakar da kashi biyu cikin ɗari, yayin da City ta ƙara nata da kimanin kashi 5.

No comments