Daga Zailani Mustapha Bisa ga irin gagarumar gudummawar da yake bayarwa wajen inganta rayuwar matasa da mata, Shikh Ibraheem Zakzaky ya sam...
Daga Zailani Mustapha
Bisa ga irin gagarumar gudummawar da yake bayarwa wajen inganta rayuwar matasa da mata, Shikh Ibraheem Zakzaky ya samu lambar yabo mai daraja ta "Best Philanthropic and Humanitarian Service for Development for Women's Education in the Nation 2024" ta ƙungiyar tallafawa shirin matasa da mata ta ƙasa (NYWSIF).
Sanarwar ta fito ne a wata takarda
mai É—auke da sa hannun Ambasada Abdullah Ibrahim Saraki, shugaban NYWSIF na
ƙasa.
Ƙungiyar ta yabawa Shaikh Zakzaky
bisa namijin ƙoƙarin da yake yi wajen bunƙasa ilimi da kuma da inganta rayuwar
matasa da mata a faÉ—in Nijeriya.
NYWSIF, ta kuma yaba da tsarin
jagoranci, da shiriya, da kuma gudummawar Shehin Malamin wajen yadda yake
inganta rayuwar al'umma.
A yau Laraba 29 ga watan Junairun
2025 ne ƙungiyar ta ziyarci Shaikh Zakzaky a gidansa dake Abuja domin gabatar
masa da lambar yabo a hukumance. Sun bayyana ƙoƙarin nasa a matsayin wanda ba
zai iya misaltuwa ba, sun kuma bayyana yadda sadaukarwarsa ta ƙara zaburantar
da al’umma wajen saka hannun jari a fannin ilimi da ci gaban matasa.
Ƙungiyar ta rubuta wata jimla a
cikin wasiƙar, inda ta ce "Albarka Tana Wurin Manya", wanda ke nuni
da matuƙar albarkar da suke nema a kan aikin su.
Da yake jawabi a madadin ƙungiyar,
Ambasada Saraki ya miƙa godiyar sa ga Sheikh Zakzaky "bisa gudummawar da
yake bayarwa wajen ciyar da ilimin mata gaba."
Bikin karramawar ya nuna irin
tasirin da Shehin Malamin ya yi ga rayuwar ‘yan Nijeriya da daman gaske.
A nasa jawabin, Shaikh Zakzaky ya
buƙaci ƙungiyar da ta ci gaba da kasancewa a kan gwadaben ayyukan raya al'umma
musamman matasa da mata a faɗin ƙasar nan, tare da tafiya bisa manufofinsu da
suka zayyana na samar da makoma mai kyau ta hanyar ilimi da tsare-tsare masu
kyau na ci gaba.
Kazalika
ya shawarce su da su ji tsoron Allah a dukkanin al’amuransu.
No comments