Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Muddin gwamna Umar Bago ya cigaba da tafiya haka to ba wata jam'iyyar adawa da za tai tasiri a 2027'

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar muddin gwamna Umaru Mohammed Bago ya cigaba da tafiya a yadda ya faro wajen nuna kishi da samar d...


Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewar muddin gwamna Umaru Mohammed Bago ya cigaba da tafiya a yadda ya faro wajen nuna kishi da samar da sabuwar jihar Neja, to babu wata jam'iyyar adawa da za tai tasiri a babban zaben 2027. Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP a karamar hukumar Chanchaga,  kuma jigo a jam'iyyar APC a yanzu,  Alhaji Hamza Yanga Buba ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yin sharhi ga yadda wasu jiga jigan PDP ke barin jam'iyyar.

Alhaji Yanga yace kwanakin baya wanda yazo na biyu a zaben kujerar gwamna a jihar nan,  Alhaji Isah Liman Kantigi,  ya bayyana ra'ayinsa dangane da irin jagorancin gwamna Umaru Bago,  kuma ka ga a wannan satin tsohon dan majalisar tarayya,  kuma wanda ya taba nuna sha'awarsa ga yin takarar kujerar gwamna a jam'iyyar PDP,  Hon. Sani Idris Legbo Kutigi ya fice daga PDP din,  wannan na nuna cewar wadanda suka san ma'anar sauyi da samar da cigaban jiha, sun gamsu da kamun ludayin gwamnatin nan.

Ba na jin maganar tazarcen Umaru Bago za ta zo da matsala, domin ba na tunanin akwai wani dan adawar da adawarsa za tai tasiri ga al'ummar jihar nan.

Idan ka dubi gwamna Umaru Bago a shekaru, idan ka kwatanta shi da shekarun mu ko a tafiyar siyasa yaro ne,  amma tunanin sa da kwakwalwarsa ta manya ce.

Kowani dan siyasa kan ce zai dora a inda aka tsaya, amma shi ya koma baya ne da nisa inda ya cigaba da ayyukan gwamnatin marigayi Abdulkadir Kure,  wanda shekara daya da watanninsa akan karagar mulkin jihar nan,  duk wanda yasan me cewa cigaba dole ya yiwa al'ummar Neja sambarka.

Saboda haka,  ina jawo hankalin masu ruwa da tsaki a jihar nan, darajarsu a wurin talakawan jihar nan shi ne marawa gwamnatin Umaru Bago baya.

Yanga Buba,  ya nemi yan majalisun tarayya da na jiha da sauran masu rike da madafun iko da su zama silar samun nasarar gwamnatin nan,  ta hanyar baiwa kudurce kudurcen gwamna Umaru Bago goyon baya,  da kuma jajircewa wajen tabbatar sun yi koyi da irin salon mulkin shi, ga al'ummar da suke wakilta.

Kudurin Umaru Bago shi ke kyautata rayuwar al'umma, inganta aikin gwamnati da yunkurin samar da sabuwar jihar Neja wadda za ta zama abin alfahari a gaba. Karkaru da biranen jihar nan duk inda ka ratsa idanun ka zai shaida ma irin cigaban da aka samu.

Bayan ficewar Hon. Sani Idris Legbo Kutigi daga PDP,  inda tabbacin kafin 2027 jam'iyyar APC za tai cikar dango ta yadda murkushe adawa baki daya. Wadanda suka rage a PDP yanzu daman su ne suka gina mata kabarin da zasu rufe ta, domin salon siyasar su ba ta cigaban kasar ba ne, yan kwashe kafa ne da yunkurin azurta kan su da dukiyar jama'a. 


No comments