Daga Awwal Umar Kontagora Mai martaba sarkin Minna, Dr. Umar Faruk Bahago ya karrama shugabannin fulani da sarautun gargajiy...
Daga Awwal Umar Kontagora
Mai martaba sarkin Minna, Dr. Umar Faruk Bahago ya karrama shugabannin fulani da sarautun gargajiya. Sarautun wanda ya hada da Janwuron Minna, wato shugaban sarakunan fulanin masarautar wanda aka nada Hon. Umar Ahmed Rebe, kwamishina jin dadin makiyaya da manoma na jihar Neja, sai Alhaji Hassan Usman Shiroro ( Garkuwan Wuro Maliki) Kodinetan Bago Ruga Ruga na jihar Neja da aka nada a matsayin Wakilin fulanin masarautar Minna.
Nadin wanda ya gudana safiyar Lahadi biyu ga watan febrairun 2025 a fadar sarkin na Minna.
Tunda farko a bayanin Mai martaba sarkin Minna, yace juriya da jajircewa, hakuri, gaskiya da rikon amana da sauraren jama'a suke tabbatar nagarta da shugabanci na gari.
Dan haka, ya nemi wadanda suka samu wannan karramawar da su tabbatar wani nauyi ne masarautar ta kara dora masu bisa ga wanda ke kan su na jagorantar al'umma.
Mai martaba ya jawo hankalinsu da su tabbatar sun yi anfani da fikira da dubaru wajen hada kan al'ummar fulani musamman dan samun zaman lafiya, hadin kai tsakaninsu da sauran al'ummar masarautar.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan nadin na sa, Jonwuron Minna, Hon. Umar Rebe, ya bayyana farin cikin sa da wannan karamcin da masarautar Minna tai masa. Yace wannan karin aiki ne bisa ga wanda gwamnatin jiha bisa jagorancin babban manomin jiha, gwamna Umaru Mohammed Bago ya dora masa na jagorantar sabuwar Ma'aikatar kula da jin dadin manoma da makiyaya na jiha.
Yace a matsayin sa na Jonwuro zai tabbatar ya cigaba da hada kan sarakunan fulanin da ardo-ardo da ke karkashin masarautar Minna dan ganin an samar da fahimtar juna tsakanin su da abokan zaman su.
Duk wasu matsalolin da ke tasowa da ke barazana ga zaman lafiya a masarautar Minna tsakanin manoma da makiyaya da sauran jama'a zamu tabbatar mun samar da mafita akan su duba da yazo daidai da kudurin gwamnatin jiha na samar da zaman lafiya da kawo karshen duk wani sabanin da ke kawo tunzuri a tsakanin al'ummar jihar nan.
A nasa jawabin kuwa, Wakilin fulanin Minna, Alhaji Hassan Usman Shiroro, ya yabawa gwamnatin jiha bisa baiwa al'ummar fulani damar da damawa da su a gwamnatance tare da cika alkawalin kafa ma'aikata dan jin dadin manoma da makiyaya a jihar Neja, wanda kuma kwamishinan ta na farko cikakken bafillatani ne.
Hassan Shiroro, yace sakamakon wannan damar da gwamnatin jiha ta baiwa fulani ya janyo dukkan nasarorin da gwamnatin jiha ke samu, da yardar Allah za mu yi anfani da wannan damar wajen kara daga darajar masarautar Minna da jihar Neja baki daya.
Kamar yadda muka goyi bayan gwamna Umaru Bago a zaben 2023, ba zamu ja baya ba, za mu cigaba da anfani da lokacin mu da abin hannun mu wajen bada gudunmawa dan cigaban gwamnatin Umaru Bago da masarautar Minna.
Kudurorin gwamnatin nan abin a yaba ne, domin Kudurori ne da zasu haifar da da mai ido da zasu kawo mana cigaban da muka dade da burinsa a jihar nan.
Alhaji Salihu Mohammad Alfa, shi ne babban sakataren ma'aikatar jin dadin manoma da makiyaya. Yace cikin watanni sha bakwai da kafuwar wannan ma'aikatar an samu nasarori masu din bin yawa da yakai yau ana karrama shugabannin fulani a jihar Neja.
Maganar rikicin manoma da makiyaya ba sabon abu ne, domin manomi da makiyayi kamar harshe ne da hakuri, dole a samu sabani da juna, amma hakan ba zai kawo hankali ya gushe ba, dole mu dawo kan tsarin mu na gargajiya idan matsala ta taso shugabannin da sarakuna su sulhunta, manoma sun kwashe dazuka, sun mayar da noma har akan labuka, yadda ba za a bar noma ba, haka ba za a bar kiwo ba, domin manomi da makiyayi kamar Hassan ne da Hussaini.
Saboda haka, mutunta juna, da nuna muhimmancin zaman tare shi zai kawo karshen kowace irin kullalliya wadda za ta kawo mana cigaba a tsakanin mu.
Taron dai ya samu wakilcin gwamna Umaru Mohammed Bago, wanda mataimakin gwamna, Kwamred Yakubu Garba ya wakilci gwamna, yayin da shugabannin kungiyoyin fulani na kasa da jiha da sarakunan fulani daga sassan kasar nan da jiha suka halarta.
No comments