Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An nemi Gwamna Umaru Bago Da Ya Samarwa Al'ummar Minna Ruwa Sakamakon Ɗaukewar Ruwan Famfo

Daga Awwal Umar Kontagora   An nemi gwamna Umaru Bago da ya samarwa al'ummar cikin garin Minna ruwa sakamakon daukewar ruwan...

Daga Awwal Umar Kontagora 

An nemi gwamna Umaru Bago da ya samarwa al'ummar cikin garin Minna ruwa sakamakon daukewar ruwan fanfon sakamakon mawuyacin wahalar ruwa da ake fama da shi. 

Wani jigo a jam'iyyar APC,  Alhaji Muhammad Lawal Ibrahim ( Hamdala) ne yayi kiran lokacin da yake zantawa da manema labarai yammacin lahadin makon da ya gabata. 

Hamdala, yaci gaba da cewar yanzu ruwan anfanin gida na hana da damar magidanta sukuni, kuma har yanzu hukumar da ke samar da ruwa cikin garin Minna ba tai wani katabus ba sakamakon rashin ruwan da ake fama da shi,  su kan yan baron ruwa suna sayar da baron ruwa akan naira dubu daya zuwa dubu daya da dari biyar a wasu unguwannin kuma kafin ma mutum ya samu ruwan sai yayi jan ido sosai. 
Azumi na gabatowa, matsalar rashin ruwan nan idan ba a yi wani abu akai ba zai shafi rayuwar al'umma musamman ma a cikin ramadan. 

Ya kamata, maigirma gwamna da ya taimaka yayi wani abu akai da fitar da al'umma wannan halin rashin ruwan da ke addabar kwaryar Minna da kewaye, domin muna bukatar kulawar gaggawa sakamakon watan ramadan da ke gabatowa. 

Ibrahim Hamdala, ya shawarci gwamnan alherin da gwamnatin jiha ta saba yi a lokacin azumi na abincin da ake rabawa mabukata a samar da shi da wuri. 

Yace, mun sani gwamnan mu adalin ne mai sauraren jama'a, kuma mai tausayi, ya kamata tun da wuri a tabbatar an tanadin tallafin abincin azumi dan ragewa al'umma radadin rashi da suke fama da shi na tsadar rayuwa musamman a bangaren abinci da ruwan sha, inji shi. 

Hamdala, ya yabawa gwamnatin jiha bisa jajircewa a wajen ayyukan raya kasa wanda dole a cewa mijin iya baba, ganin yadda a kowani lungu da sako ake gudanar da ayyukan, amma duk da hakan a cikin ido ake tsawurya, talakawa na cikin halin kunci na rashi da tsadar rayuwa wanda suna bukatar kulawar gwamnati cikin gaggawa.

No comments