Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Honorabul Aminu Yunusa Ya Zama Mainan Marmara

Daga Idris Umar Zariya   A ranar Asabar 1/2/25 ne mai girma Sarkin Marmara Alhaji Musa Adamu ya naÉ—a Honorabul Aminu Yunusa a ma...

Daga Idris Umar Zariya 

A ranar Asabar 1/2/25 ne mai girma Sarkin Marmara Alhaji Musa Adamu ya naɗa Honorabul Aminu Yunusa a matsayin Mainan Marmara dake ƙaramar hukumar Sabon Gari jihar Kaduna.

Wakilinmu na cikin wakilan kafafen yaÉ—a labarai da suka sami shaida yadda taron ya gudana.

Taron an gudanar da shi ne a ƙofar fadar Sarkin na Marmara dake Sabon Gari.

Kafin gudanar da naÉ—in majalisar Sarkin Marmaran sun tarbi manyan baki da suka Marawa naÉ—in baya.

Daga cikin su akwai zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari kuma shugan kungiyar ciyamomin jihar Kaduna (ALGON) Chiarman Honorabul Abubakar Jamilu Albani Samaru da Honorabul Datti Muhammad Babawo da Ambasada suke Buba.dukkansu sun shaida naɗins Honorabul Aminu Yunusa a matsayin Mainan Marmara.

Hajiya Maimuna itace mahaifiyar shi Mainan Marmaran a zantawarta da manema labarai tayi fatan Allah ya sanyawa wannan matsayi da ÆŠanta ya samu kuma tayi ad'du'ar Allah ya sakawa Sarkin Marmara da alheri da ya baiwa Aminu Yunusa wannan matsayi.

Haka zalika babban yayansa Hajiya Fatima itama ta yi fatan alheri da wannan karamci da ƙaninta ya samu.

Hajiya Zakiyya Aminu Yunusa na daga cikin matansa ita ma ta yi fatan Alheri ga samun wannan matsayi na Mainan Marmara da mai gidansu ya samu ta ce Allah ya taya shi riko kuma tayi addu'ar Allah ya maida kowa gidansa lafiya.

Daga ƙarshen taron Mainan Marmaran ya yi jawabin godiya ga dukkan wanda suka zo taya shi murna kuma ya yi jinjina ga mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli da majalisar masarautar Zazzau da Hakimai da dukkan mutane ƙaramar hukumar Sabon Gari da jami'ar anguwa Marmara baki ɗaya.

Mawaƙa da masu wasan ƙwaikwayo da kungiyoyine suka gudanar da wasanni ciki har da Malam gundura da abokinsa sankace.

An yi taro lafiya an tashi lafiya.

No comments