Daga Awwal Umar Kontagora A karon farko ruggar Jita Kangon Fulani da ke gundumar Maikunkele a masarautar Minna ya samu masalla...
Daga Awwal Umar Kontagora
A karon farko ruggar Jita Kangon Fulani da ke gundumar Maikunkele a masarautar Minna ya samu masallacin juma'a na farko bisa karo karon da al'ummar ruggar suke yi dan cigaban rayuwarsu.
Masallacin juma'ar wanda, Sheikh Kamilu Abubakar Minna ya jagoranci bude wa tare da jagorantar sallar juma'ar, an fara aikin da kammala aikin cikin shekara daya da farawa.
Da yake jawabi ga wakilin jaridar Madogara, Dagacin Maikunkele ta Arewa, Alhaji Ibrahim Isah yace ina godiya ga Allah bisa fahimtar zaman lafiya tsakanin al'ummar wannan yankin na nada sarkin fulani, Dikko Nurudden Muhammad, bayan nadin bisa kokarin jama'ar wannan yankin yau mun bude masallacin juma'a na farko da suka gina.
A madadin Hakimin da Mai martaba sarkin Minna, Dr. Umaru Faruk Bahago, ina kara jawo hankalin su akan hadin kai, zaman lafiya da juna da sauran kabilun Gwarawa da Hausawan da suke zagaye da su.
Dikko Nurudden Muhammad, sarkin fulanin Jita Kango, ya godewa yan uwa da abokan arziki da suka tara taro, sisi har aka cin ma wannan nasarar.
Dikko Nurudden, yace asalin wannan wajen iyayen mu ne suka kafa shi yau sama da shekaru saba'in da suka gabata. Amma duk da goyon bayan da muke baiwa gwamnati ba mu taba samun wani cigaba daga bangaren gwamnati na abinda ya shafi morewa rayuwar al'umma ba.
Ba mu da makarantar boko, ba mu da asibiti, ba mu da ruwan sha, babban matsala ma ba mu da hanya.
Duk yawan ruggar da ke tattare da jama'a da dama fanfon burtsatse daya muke da shi wanda hukumar UNICEF tai mana shekaru talatin da suka gabata. Yanzu haka muna wani karamin Dam da dabbobin mu ke shan ruwa, amma kimanin shekara uku da ya gabata mu ne muka yi karo karon fara yashe shi amma daga karshe abin yafi karfin mu.
Muna kira ga adalin gwamna, babban manomin jiha, Umaru Mohammed Bago da ya dubi al'ummar Jita Kango Kasancewar dan uwan mu bafillatani mai kishin fulatanci da a samar mana da makarantar Nomadic dan yayan mu su yi karatu, sannan akwai matsalar asibiti ga kuma na ruwan sha.
Sheikh Kamilu Abubakar Minna, ya jawo hankalin al'ummar Jita Kango da su zama masu riko da addini su tabbatar sun raya wannan masallacin.
Sheikh Kamilu, ya cigaba da cewar duk wani soyayyar da mutum zai yi ko Ibadah muddin baya cika sallah ya tabbatar yana cikin hasara, sallar juma'a tana da falala dan haka matasa su gujewa sabbin akidun da ke fada da koyarwar Annabi Muhammadu (S. A. W) duk abinda Allah ya haramta shi, to haramacce ne, haka duk abinda Allah ya halasta shi, to halastacce ne. Don haka addinin mutum baya cika sai ya cika sallarsa, idan sallah ta cika itace wajibi sunnoni da mustahabbai na iya biyo baya.
Kwamishinan ma'aikatar kula da jin dadin manoma da makiyaya, Hon. Umaru Ahmed Rebe (Janwuron Minna) da ya samu wakilcin Kodinetan ma'aikatar na karamar hukumar Bosso, Hon. Ibrahim Jikuchi ya nemi malamai da sauran al'ummar jiha da su cigaba da yiwa gwamna Umaru Mohammed Bago addu'o'in samun nasara akan ayyukan da sanya a gaba.
Janwuro, ya cigaba da cewar idan sarkin fulani, Dikko Nurudden Muhammad ya jagoranci samar da yayan makiyaya a wannan ruggar wadanda za a sanya su makarantar Nomadic da gwamnatin jiha ke kudurin samar, tabbas bada jimawa ba Jita Kango za ta samu makarantar kamar yadda suke muradi.
Kwamishinan ya nuna jin dadin sa kan yadda al'umma suka hada karfi da karfe wajen gina wannan masallacin, dan haka bada jimawa ba za mu kawo wutan solar guda biyu dan sanyawa a wannan masallacin.
Dangane da matsalar ruwan sha kuwa, bisa goyon bayan da wannan al'ummar ta bayar lokacin kidayar tantance makiyaya da dabbobin su, muna bakin kokarin mu na ganin mun samar fanfon burtsatse mai aiki da hasken rana bada jimawa ba.
Taron bude masallacin juma'ar dai ya samu halartar manyan malaman tijjaniya musamman almajiran Sheikh Dahiru Usman Bauchi da sauran sarakunan fulanin daga sassan jihar Neja.
No comments