Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ba Zan Yi Musayar Yawu Da Nasir El-rufa'i Ba - Daga Nuhu Ribadu

An ja hankalina  zuwa ga hirar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya yi da kafar yada labarai  da yammacin rana...

An ja hankalina  zuwa ga hirar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya yi da kafar yada labarai  da yammacin ranar Litinin.

Da ba don gudun kada na yi shiru a gaskata maganganunsa ba, da na yi watsi da shi. Saboda na fi shagaltuwa da tarin aiyukan da ke gabana,fiye da tanka ire-iren su  Nasir El-Rufai a kafafen yada labarai.

Duk da cin zarafi da aibata ni da Nasiru yake yi, hakan bai sa na taba fadin wani mummunan abu akansa ba a ko’ina. Ba don komai na ki aibata shi ba sai don  mutunta zumuncin da ke tsakaninmu da kuma abotar mu ta baya, don haka abinda ban yi tun a baya ba, ba zan fara yanzu ba.

Sai dai ina kira ga jama'a da su yi watsi da ikirarin El-rufai akaina

Bari na kankare muku shakku in fadi da babbar murya cewa ban taba tattauna batun ko zan yi takarar shugabancin kasa a shekarar 2031 da kowa ba, domin hankalina da gangar jikina sun ta'allaka ga aikina na ganin ci gaban Najeriya da nasarar gwamnatin shugaba Tinubu.

Don haka ina rokon Nasir El-Rufai da ya bar ni na ci gaba da fuskantar aikina na gina kasa kamar  yadda ban dame kaina da al'amuransa ba.

-Nuhu Ribadu

No comments