Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Ƴan Kasuwar Neja Su Goyi Bayan Ƙudurorin Gwamnatin Jiha Na Karya Farashin Kayan Abinci'

Daga Awwal Umar Kontagora   An nemi yan kasuwar Neja da su goyi bayan Kudurorin gwamnatin jiha na karya farashin kayan abinci mu...

Daga Awwal Umar Kontagora 

An nemi yan kasuwar Neja da su goyi bayan Kudurorin gwamnatin jiha na karya farashin kayan abinci musamman duba da lokacin azumin ramadan mai zuwa domin al'umma su samu saukin rayuwa. 
Shugaban kungiyar masu fadakar da maniyyata da aikin Umrah, Sheikh Muhammadu Liman Masha'Allahu ne yayi kiran bayan wani zama da gwamnatin jiha ta yi da malamai kan shirye shiryen tunkarar azumin ramadan mai zuwa. 

Masha'Allahu, ya ce kamar yadda gwamna Umaru Mohammed Bago yace zai samar da tirela dubu daya na abinci dan karya farashin abinci, idan shugabannin kananan hukumomi zasu koyi da hakan, yan kasuwa ma su goyi bayan hakan, ina tabbacin za a yi azumin bana cikin sauki. 
Da ya juya kan tsinuwar da gwamna Umaru Mohammed Bago yayi kan wadanda ke karkatar da alheran da gwamnati ke yiwa talakawa kuwa, Shehin malamin yace addu'ar shugaba karbabbiya ce. A shekarar da ta gabata gwamnatin jiha ta bada abinci a rabawa talakawa, amma wasu marasa amana suka karkatar da shi. A wannan karon gwamna yace zai zaftare farashin abinci ne, inda yayi alkawalin kawo tirela dubu daya na abinci wanda za a sayar da shi ga al'umma, ta yadda jama'a zasu iya sayen abinci cikin saukin farashi albarkacin watan ramadan wannan yanayin da kudurin da gwamna ke da shi na tausayawa talakawan sa abin mu yaba ne. 

Malamin ya gargadi wadanda gwamnati za ta damkawa wannan amanar da su ji tsoron Allah, su sauke nauyin da amanar da za a ba su. 

Malamin, ya bayyana cewar za mu yi anfani da wannan lokacin har farko da karshen ramadan da yiwa gwamna Umaru Bago addu'o'in samun nasara. 

Saboda haka, ina jan hankalin al'umma da su kara hakuri da yin fatan alheri ga gwamnatin Umaru Bago domin yana da kudurin alheri a jihar nan. 

Suma yan kasuwa suna da rawar takawa gaya, musamman idan sun yi koyi da irin wannan aikin alherin na gwamna Umaru Bago wajen zaftare farashin kayayyaki a kasuwanni a lokacin wannan watan na ramadan, zasu ga albarka da nasarori a kasuwancin su idan sun yi hakan. 

Da ya juya kan masu hannu da shuni kuwa, yace kar su ji gwamna ya bullo da wannan su fasa bada tallafin da suka saba bayarwa ga marasa galihu, domin kowa ana bukatar yayi anfani da wannan lokacin wajen samun ladaddakin da Allah ke baiwa masu bayarwa da sanya farin ciki ga marasa galihu.

No comments