Daga Awwal Umar Kontagora An shawarci gwamnan Neja, Hon. Umaru Mohammed Bago da ya kara kwazo akan ayyukan da sanya a gaba na ...
Daga Awwal Umar Kontagora
An shawarci gwamnan Neja, Hon. Umaru Mohammed Bago da ya kara kwazo akan ayyukan da sanya a gaba na inganta sabuwar jihar Neja. Domin duk mai hankali idan ya shigo jihar nan ya san da cewar yanzu ne aka samu zababbiyar gwamnati wanda jama'a suka zaba da hannunsu kuma ta tabbatar da kafa turbar da jama'a suka dade suna burin samu.
Ayyukan da gwamnatin ta sanya a gaba ayyuka ne da ke bukatar kudaden shiga dan sauke wannan nauyi da kokarin tabbatar da inganta rayuwar al'umma. Saboda haka jihar Neja na bukatar karin hanyoyin kudaden shiga da za ta samu damar cika wannan kudurin. Muna da hanyoyi da dama da idan aka waiwaye su cikin kankanin lokaci za a samu biyar bukata.
Tarihin kafuwar kasar nan ba zai tabbata sai an kalli gudunmawar da jihar nan ta bayar musamman kan shugabanci da aza turbar da marasa kishin kasa suka watsar, wanda a yanzu mun samu jarumi cikakken mai kishi da yake kokarin dawo da shi a jihar nan.
Kamar yadda maigirma gwamna ya karbi rahoton sabunta Gurara Dam, a wannan namijin aikin a tabbatar an samar da masaukan baki dan ragewa birnin tarayyar kasar nan cinkoso, sannan a samar da hanyar jirgin kasa da zai bulla Mutum Daya, wanda hakan zai farfado da kauyukan da ke yankin, kasuwanci zai bunkasa kuma za a saukaka zurga zurga a wannan bangaren.
Bayan nan, gwamnatin jiha ta tabbatar ta samar da wani hanyar jirgjn kasa wanda zai tashi daga Gurara zuwa Zunguru da ake cewa Zungeru a yanzu, domin Zunguru wurin tarihi ne da ya samar da shugabannin da suka fara jagorantar kasar nan bisa jagoranci na gari irin su marigayi Nnamdi Azikwe da makamantan su, kuma gwamnatin Umaru Bago ta tabbatar cibiyar tunawa da marigayi Nnamdi Azikwe da aka fara ginawa a shekaru da dama kuma aka yi watsi da shi ta kammala shi, wannan zai baiwa yan yawon bude ido damar shigowa dan kafa abubuwan cigaba a jihar nan.
Dan haka, idan gwamna Umaru Bago zai kara himma wajen cigaba da sauraren shawarwari nagartattu kuma yayi aiki da su, ina da tabbacin tarihin ba zai goge ba ko bayan baya doron duniya, domin mun gamsu da irin kudurce kudurcen shi na cigaban jihar nan.
Dattijon dan siyasar ya yabawa gwamnatin kan irin yadda ta jajirce ba dare ba rana wajen ganin ayyukan da ta sanya a gaba ba a yi ma ta zagon kasa ba.
Haka, ya shawarci makusantan gwamnan da cewar kar su dubi abinda zai shiga aljihunsu ko dan tarawa iyalansu, domin idan suka bada gudunmawa wajen ganin wannan ayyukan da gwamnatin ta sanya a gaba sun samu nasara, to nasarar ba ta shi bace shi, ta su ce baki daya, kuma abinda suke tsoro na rayuwa, Allah zai cigaba da shiga lamarin su.
Amma tabbas, idan aka waiwayi wuraren tarihi aka samar da kyakkyawar tsari, za a samu cigaba da kuma karin hanyoyin kudaden shiga ba tare da an dogara da ma'adanan kasa ba, ko tallafi daga gwamnatin tarayya ko kasashen ketare ba.
No comments