Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Kebbi ya ƙaddamar da sabon ɗakin wasan ƙwallon Badminton tare da jaddada ƙudurin sa wajen taimakawa harkokin wasanni a jihar

Daga Awwal Umar Kontagora   Gwamnan Kebbi Kwamared Dakta Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) ya kaddamar da ɗakin wasan ƙwallon Badminto...

Daga Awwal Umar Kontagora 

Gwamnan Kebbi Kwamared Dakta Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) ya kaddamar da ɗakin wasan ƙwallon Badminton a garin Birnin Kebbi tare da jaddada ƙudurin sa na cigaba da taimakawa cigaban harkokin wasanni a jihar.

Gwamnan ya kaddamar da dakin wasar ne a garin Birnin Kebbi. Dakin wasan na Badminton da ya kaddamar shi ne irinsa na farko a jihari dama arewa maso yammacin Nijeriya.

Da yake jawabi a lokacin ƙaddamar ɗakin wasan, gwamnan ya bayyana ɗakin wasan a matsayin wani cigaba gagarumi da aka samu a harkar wasannin jihar Kebbi.

Gwamnatin Kebbi ce ta ɗauki nauyin gina wannan ɗakin wasan bayan da aka dade ana neman gina wannan wuri domin samar da ɗakin gudanar da wannan indoor games na zamani a jihar.

Gwamnan ya ƙara da cewar yanzu jihar Kebbi ta zamo abin alfahari a cikin tsaran ta bisa samun wannan ɗakin wasan na zamani inda gwamna yayi alƙawarin gina irin wannan ɗakin wasan a fadin jihar baki ɗaya domin inganta harkokin wasanni a jihar.

Gwamna Nasir Idris shi ma ɗaya ne daga cikin masu buga wasar Badminton kuma uban kungiyar masu buga wasar Badminton na jihar Kebbi.

Gwamnan ya ƙara da cewar wasar Badminton wasa ce da take samar da haɗin kai, soyayya da bunƙasa tattalin arziki da cigaban al'umma inda yace gwamnatinsa za ta cigaba da bayar da goyon bayan ta da gudummawar ta ga harkokin wasannin Badminton domin ɗaga darajar wasar da cigaban ta.

Ya gaba da cewar saboda rashin ɗakin wasan ƙwallon Badminton a can baya, wasar cin kofin ƙauran Gwandu a Abuja ake gudanarwa, amma gasar ta bana a nan Birnin Kebbi za'a gudanar da ita saboda samun wannan dakin wasan na zamani.

Gwamnan ya umarci masu shirya gasar, dasu fara shirye-shiryen gudanar da gasar na wannan shekarar inda yace jihar Kebbi zata cigaba da kasancewa ɗaya daga cikin jihohin da suka shahara a harkar wasannin Badminton da sauran wasannin motsa jiki.

A na shi jawabin, Kwamishinan ayyuka na jihar Kebbi Injiniya Abdullahi Musulmi, ya yabawa gwamnan bisa irin gudunmawa da goyon bayan da yake baiwa harkokin wasannin motsa jiki musamman kwallon Badminton a jihar Kebbi.

 Ya cigaba da cewar irin yadda jihar Kebbi ta shahara matuƙa wajen wasar Ƙwallon Badminton inda jihar ta samar da shahararren ɗan wasan Badminton irin Fatauci.

Yace gasar bana da za'a shirya kuma a gudanar a cikin wannan sabon ɗakin wasan, za ta kara samar da haɗin kai da kuma ɗaga darajar jihar Kebbi a harkokin wasanni.

Shi ma shugaban ƙungiyar ta kwallon Badminton wato CSDP Badminton Club, Alhaji Zubairu Sidi, yayi godiya da jinjina ta musamman ga gwamna Kwamared Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu bisa irin kyawawan shugabancin da yake gudanarwa a jihar Kebbi tare da tabbatar ma cewar zasu kula da wannan dakin wasan ƙwallon Badminton kamar yadda ya kamata domin ɗaga darajar harkokin wasannin Badminton a jihar, Najeriya dama Afrika baki ɗaya.

Haka kuma yayi godiya ta musamman ga Injiniya Abdullahi Umar Muslim bisa irin kokari da gudummawar da yake baiwa harkokin wasan ƙwallon Badminton dama kungiyar ta wasan kwallon Badminton ta jihar Kebbi.

A lokacin ƙaddamar da dakin wasan,  kungiyar Ƙauran Gwandu Youth Academy ta gudanar da wata ƙayatattar wasa a wurin.

An gabatar da kyaututtuka daban-daban ga maigirma gwamna bisa irin gudunmawar da yake baiwa harkokin wasan ƙwallon Badminton a jihar Kebbi.

No comments