Daga Awwal Umar Kontagora A cigaba da zagayen godiyar da Gwamna Kwamared Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu ke yi a jihar Kebbi, ...
A cigaba da zagayen godiyar da Gwamna Kwamared Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu ke yi a jihar Kebbi, kan zaɓen da aka yi masa a shekarar 2023 a matsayin gwamnan jihari, ɗaruruwan ƴaƴan jam'iyyar PDP ne sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a lokacin da gwamnan yakai ziyarar godiya a ƙaramar hukumar mulki ta Yawuri ranar Alhamis din makon nan da ya kare.
Yayan PDP din da suka sauya sheƙar tare da sanannun jagororin jam'iyyar PDP na ƙaramar hukumar mulkin Yawuri sun dinga kirarin "Ƙauran Gwandu Alheri ne" tare da nuna goyon bayan su ga gwamnatin Ƙauran Gwandu.
A lokacin da suke jawabin dalilin sauya sheƙar su zuwa Jam'iyyar APC, wasu daga cikin jagororin jam'iyyar ta PDP da suka haɗa da: tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Kebbi mai wakiltar ƙaramar hukumar mulki ta Yawuri Alhaji Shehu Aliyu (Marafan Yawuri), da Alhaji Audu Maigandi (Jarman Yawuri) da Alhaji Abbas Gulma sun bayyana cewar sun koma jam'iyyar APC ne bisa adalci da kyakkyawan shugabanci irin na Gwamna Nasir Idris Ƙauran Gwandu.
Haka kuma sun bayyana cewar yana daya daga cikin dalilan su na sauya sheka zuwa jam'iyyar APC saboda irin yadda gwamnan yake cigaba da gudanar ayyukan alheri da cigaban al'umma a ko'ina a faɗin jihar musamman raya karkara da birane.
Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kebbi, Hon. Abubakar Kana Zuru ne ya karɓi masu sauya sheƙar inda ya gabatar da su ga gwamnan tare da basu tabbacin za'ayi musu adalci da kuma ba su cikakkiyar dama na sauran ƴaƴan jam'iyyar ta APC.
Da yake cigaba da jawabi a lokacin karɓar masu sauya sheƙar, Alhaji Abubakar Kana Zuru ya bayyana cewar wannan sauya sheƙar da suka yi zuwa jam'iyyar APC kamar sake dawo gidan su na ainihi ne domin dama ƴaƴan jam'iyyar APC ne kafin wani dalilin yasa su bar jam'iyyar zuwa jam'iyyar adawa take PDP, inda yace dama su ƴan cikin gida ne a jam'iyyar APC.
Haka kuma a lokacin ziyarar godiyar, kwamishiniyar ilimin jihar Kebbi, Dakta Halima Muhammad Bande da shugaban hukumar ilimin bai ɗaya na jihar Kebbi wato SUBEB, Farfesa Khalid Suleiman Jega sun zayyano irin ayyukan alheri da gwamnan ya gudanar a ɓangaren ilimi a masarautar Yawuri.
Dakta Halima Bande ta bayyana cewar makarantu saba'in da tara ne waɗanda suka haɗa da firamare da sakandare gwamnatin Kauran Gwandu ta gyara ko gina sabbi a masarautar Yawuri inda yanzu haka guda sittin ana cigaba da aikin gyaran su.
Dakta Bande ta bayyana cewar gwamna ya cigaba da biyan kudin jarabawar WAEC ga ɗaliban sakandare da ke ajin karshe inda ta kara da cewar a ƴan kwanakin nan ma gwamnati ta amince da biyan kudin jarabawar WAEC na shekarar 2025.
Haka kuma, ta ƙara da cewar domin magance matsalolin rashin isassun kwararrun malaman makaranta, maigirma gwamna ya amince da daukar sabbin kwararrun malaman makaranta guda dubu biyu a faɗin jihar.
Dakta Halima ta cigaba da cewar Maigirma gwamna ya baiwa makarantar sojoji ta command school ta mata da ke Goru da ta maza da ke Jega, gudunmawar naira miliyan hamsin ga makarantar matan da kuma naira miliyan talatin ga makarantar mazan.
Haka a wurin taron, sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Yakubu Bala (Tafidan Yawuri) ya bayar da kyautar mota da babura ga dukkanin shugabannin jam'iyyar APC na gundumomin ƙaramar hukumar guda goma, da sakataren jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar mulki ta Yawuri da shugaban matasa da kuma shugabar matan jam'iyyar ta APC na ƙaramar hukumar mulki ta Yawuri domin nuna godiyar sa gare su bisa irin goyon bayan da suke ba shi da kuma gwamnatin Kauran Gwandu da jam'iyyar APC.
No comments