Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

MAN Ta Kasa Ta Tsawaita Rikon Kwarya Ga Hon. Yusuf Mani Na Watanni Shida

Daga Awwal Umar Kontagora   Bayan Æ™arewar wa'adin kwamitin riÆ™o na Æ™ungiyar MAN (Miners Association Of Nigeria) reshen jihar...

Daga Awwal Umar Kontagora 

Bayan ƙarewar wa'adin kwamitin riƙo na ƙungiyar MAN (Miners Association Of Nigeria) reshen jihar Neja da kuma bukatar sake tsarawa tare da sake fasalin tafiyar da kungiyar reshen jihar Neja dan tabbatar da sabunta haɗin gwiwa tsakanin yayan ƙungiyar da gwamnatin jihar Neja domin cigaban da ake samu a fannin sana'ar ma'adanan kasa.

Shugaban kungiyar ta kasa, Dele Ayanlekan ya amince da karin wa'adin shugabancin rikon kwaryar saboda bukatar kawo canje canje da samar da sahihiyar jagorancin kungiyar a jihar Neja. 

Bayanin hakan na kunshe ne a wata takardar tabbacin karin wa'adin da sakataren kungiyar ta kasa, Suleiman Liman ya sanyawa hannu, inda takardar ta bada tabbacin karin wa'adin ga shugaban na riko,  Alhaji Yusuf Mani na tsawon watanni shida. 

An tsawaita wa'adin kwamitin riÆ™on ne na tsawon watanni shida, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Disamba, 2024. Ana sa rai da fara ayyukan kwamitin riÆ™on ne daga ranar 30 ga watan Mayu, 2025, sannan ta miÆ™a wa kwamitin zaÉ“e wanda hukumar ta Æ™asa za ta kafa nan gaba kadan. 

Da yake amsa tambayoyin jaridar MADOGARAR Labarai, jami'in yada labarai na kungiyar reshen jihar Neja, Hon. Uba Usman ya tabbatar ma wakilin mu samun takardar daga sakatariyar kungiyar ta kasa. Inda ya kara da cewar takardar ta tabbatar da cigaba da jagorancin kungiyar a jihar Neja, tare da tabbatar da duk yan kwamitin da aka zaba suna nan akan matsayin su, sai dai takardar ta baiwa kwamitin rikon damar kara wasu idan bukatar hakan ta taso saboda samun damar kammala ayyukan da aka dora masu cikin wannan lokacin. 
Hon. Uba, ya kara da cewar akwai wasu muhimman ayyukan da aka dorawa kwamitin zuwa yanzu da ya hada da kawo dukkan masu haÆ™ar ma'adinai, dillalan kayayyakin ma'adinai da masu ba da shawara, da sauran waÉ—anda ke Æ™arÆ™ashin Æ™ungiyar MAN jihar Neja wuri daya. 

Tare da sake tsara rajistan duk masu aikin haÆ™ar ma’adinai zuwa Æ™ungiyoyin haÉ—in gwiwa ( Cooperative) na mambobi mafi Æ™arancin mutum biyar, da tabbatar da sun sami takardun ma’adinan da suka dace, sannan a yi musu rajista a cikin Æ™ungiyar ma’adanai ta Nijeriya a sakatariyar ta Æ™asa.

Bayan nan takardar ta nemi kwamitin rikon kwaryar da ta tabbatar ta samar da haɗin kai da ma'aikatun tarayya, na jihohin da abin ya shafa dan inganta haɓakar ma'adanai.

Bayan nan an bukaci kwamitin da shirya jerin sunayen ‘yan takarar da suka yi rajista a duk Æ™ananan hukumomin jihar da ake gudanar da ayyukan haÆ™ar ma’adinai.

Sannan su tabbatar da haɗa kai da yin gamayya da hukumomin tsaro da abin ya shafa, domin kawo ƙarshen matsalar haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba da ta'addanci a cikin jihar.

Uwar kungiyar ta kasa ta bukaci karfafa ma'aikata dan kiyaye ayyukan haƙar ma'adinai masu aminci ta hanyar shirya wayar da kan jama'a da kuma bin ka'idojin muhalli, lafiya da aminci da bin dokokin da gwamnati ta tsara.

Tabbatar da duk masu aikin haƙar ma'adinai suna kula da kyakkyawar alaƙa tare da al'ummomin da suka karɓi bakuncinsu ta hanyar aiwatar da aminci na wa'adi da sharuɗɗa a cikin Yarjejeniyar cigaban al'umma bisa tsarin (CDA) da mutunta sauran haƙƙoƙin jama'a bisa tsarin (CSR) da ke fitowa daga al'ummominsu.

Haɗa kai da hukumomin da suka dace na gwamnatin jiha dan jaddada ayyukan haƙar ma'adinai, masu haƙƙin haƙar ma'adinai ta hanyar tallata haƙƙin haƙar ma'adinai ta hanyar ba da shawarwarin da gwamnatin jiha za ta iya bugawa.

Kungiyar ta kasa ta baiwa kwamitin rikon shawarar bin tsarin tafiyar da harkokin kuÉ—i da kuma yadda ya kamata a tura kason tarayya na  kuÉ—aÉ—en shigar da ake samu uwar kungiya ta Æ™asa da sashin jiha ke samarwa.

Takardar amincewar karin wa'adin ta nemi kwamitin da ta tsara rukunonin ƙungiya a kowace ƙaramar hukumar da suka dace da sakatariyar ƙasa.

 A karshe uwar kungiyar ta bayyana cewar cikin watan Afrilu 2025, ya kamata kwamitin ta sake buga buÆ™atun cancanta dan duk muÆ™aman da za a yi takara kuma a yi hulÉ—a tare da sakatariyar ta kasa.

Hon. Uba ya bayyana cewar suna da kwarin guiwar wannan damar da aka sake ba su karkashin jagorancin Alhaji Yusuf Mani kwalliya za ta biya kudin sabulu duba da irin tsare tsaren da gwamnatin jiha ta fitar tsarin ne da zai haifar da da mai ido ga kungiyar MAN reshen jihar Neja.

No comments