Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Kebbi Za Ta Kashe Miliyan Hamsin Da Huɗu Don Gudanar Da Auren Gata Ga Mutane Ɗari Uku A Karo Na Biyu

Daga Awwal Umar Kontagora   Gwamnan Jihar Kebbi Kwamared Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya amince da gudanar da bikin auren gata a ka...

Daga Awwal Umar Kontagora 

Gwamnan Jihar Kebbi Kwamared Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya amince da gudanar da bikin auren gata a karo na biyu a jihar Kebbi 

Naira miliyan hamsin da huɗu ne  gwamna ya amince da acire a matsayin kuɗin sadaki da sauran hidimomin bikin ma'auratan mutum dari uku.

Wannan shine karo na biyu da wannan gwamnatin ƙarƙashin jagorancin  gwamna Kwamared Nasir Idris Ƙauran Gwandu take gudanarwa.

Za'a gudanar da taron bikin auren gatan ne ranar 27/2/2025 a fadar Mai martaba sarkin Gwandu Manjo Janar Mohammadu Iliyasu Bashar Rtd da ke cikin garin Birnin Kebbi.

Shugaban kwamitin gudanar da auren gatan kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Kebbi Alhaji Suleiman Mohammed Argungu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake wata ganawa ta musamman da manema labarai a garin Birnin Kebbi.

A lokacin ganawar, Alhaji Suleiman Mohammed Argungu ya samu rakiyar Kwamishinan yaɗa labarai da raya al'adun jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Ahmed Bk da kuma Kwamishinan muhalli na jihar Kebbi Hon. Musa Muhammad Tungulawa.

Alhaji Suleiman Mohammed Argungu ya bayyana cewar nasarar da aka samu a shekarar da ta gabata a lokacin da gidauniyar matar gwamna wato NANAS Foundation ta jagoranci irin wannan auren ne yasa gwamnatin jihar Kebbi taga dacewar sake gudanar da irin wannan auren gatan.

Haka kuma ya bayyana cewar aƙalla angwaye da amare dari shida za'a ɗaurawa auren gatan waɗanda dukkanin su sun fito ne daga al'umma marasa ƙarfi daga sassan jihar Kebbi.

Kowace amarya zata karɓi sadakin ta na Naira dubu ɗari da tamanin (₦180,000) tare da gado da filo da sauran kayan daki.

Haka kuma shugaban kwamitin ya kara da cewar an kafa kwamitin da zasu tantance waɗanda zasu ci gajiyar shirin a dukkanin kananan hukumomin jihar guda ashirin da daya.

Kwamitin zai gudanar da tantancewar ne bisa ƙa'idojin da aka shimfida wanda suka haɗa da dole mijin ya zama yana da gidan aje matar da kuma sana'ar da zai ɗauki sauran ɗawainiyar yau da kullum na matarsa.

Haka kuma ya bayyana cewar dukkanin angwaye da amaren za'a gudanar da gwajin lafiyar su da kuma kwayar halittar su inda su kuma mata za'a kara har da gwajin juna biyu wato ciki.

Alhaji Suleiman Argungu ya ƙara da cewar za'a gudanar da wannan auren ne tsakani da Allah ba tare da nuna bambancin siyasa ba.

Bayan kammala taron ƴan jaridar, an nunawa ƴan jaridar irin kayan da gwamnatin ta sayo domin gudanar da bikin.

No comments