Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jama'a Su Baiwa Gwamnati Goyon Baya Wajen Tabbatar Da Ayyukan Hanyoyin Cikin Gari

Daga Awwal Umar Kontagora   An yi kira ga al'umma da su baiwa gwamnati goyon baya wajen ganin an cigaba da ayyukan hanyoyin ...

Daga Awwal Umar Kontagora 

An yi kira ga al'umma da su baiwa gwamnati goyon baya wajen ganin an cigaba da ayyukan hanyoyin cikin gari. Wani jigon siyasa a jihar Neja, Alhaji Hamza Yanga Buba ne yayi kiran kan turjiyar da kamfanonin da ke gudanar da ayyukan hanyoyi da magudanan ruwa na cikin unguwanni. 

Yace tun farko akwai tsarin sabunta garuruwa wanda mafi yawa wasu al'ummomi koda sun samu tsarin unguwanni idan sun shiga cikin unguwannin sai suka rika wuce iyakarsu suna fadawa hurumin da ba na su ba. 
Ya cigaba da cewar maganar gaskiya ya kamata gwamnati ta sanya idanu sosai akan ma'aikatar kula gidaje da tsarin garuruwa, domin duk wata sabuwar unguwar da aka kafa, koda an fitar da magudanan ruwa da hanyoyi suke rushe tsarin tare da baiwa masu hannu da shuni damar wuce iyakokin da suka mallaka. 
Misalin hakan ya faru a nan sabuwar shango da ake cewa Brighter, duk filayen unguwar nan ni na yankan su, kuma tun farko mun fitar da hanyoyi da magudanan ruwa, amma abin takaici, masu hannu da shuni da suka mallaki filaye cikin unguwannin nan, sun zo suna ta toshe hanyoyin da aka fitar da magudanan ruwa, yau gwamnati ta soma ayyukan hanyoyin cikin unguwanni mutane na turjiya akan an taba gidajen su. 

Akwai gurbatattun jami'ai a ma'aikatar kula filaye da gidaje wadanda dole gwamnati ta taka masu burki, domin dukkan wuraren da gwamnatin ke gudanar da ayyukan nan ana bin tsarin fasalin gari ne da ake cewa" Master Plan " saboda maganar turjiya akan neman gwamnati ta biya diyya ma kuskure ne babba. 

Yanga Buba, ya shawarci gwamna Umaru Mohammed Bago da ya cigaba da gudanar da ayyukan da ya sanya a gaba ba tare da ya tsaya saurare ko kallon idon wasu ba, in ma kuskure ne su din ne ba su abinda ya dace kafin su fara ginin su ba, balle su yi tsammanin samun wani abu da sunan diyyar fili daga hannun gwamnati ba. 

Haka kuma ya shawarci gwamnatin jiha da sanya idanu sosai duk jami'in ma'aikatar kula gidaje da filaye da samun hannun sa wajen yiwa Master Plan zagon kasa a yi mai horo mai tsanani dan su ne kan gaba wajen kawo hargitsi da cinkoso a cikin unguwanni ta hanyar bada damar ruguza tsarin gidaje da ake ginawa a cikin garuruwa.

No comments