Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar kammala ginin babbar sakatariyar ta jiha abu ne wanda yayi daidai da buƙatar yanayi...
Daga Awwal Umar Kontagora
An bayyana cewar kammala ginin babbar sakatariyar ta jiha abu ne wanda yayi daidai da buƙatar yanayin ma'aikatan jihar Kebbi.
Jihar Kebbi tana da ma'aikatan da suka kai adadin dubu ashirin da biyu, waɗanda suke aiki cikin ƙwaryar garin Birnin Kebbi, saboda haka samun yalwataccen wurin da zasu gudanar aikinsu wani abu ne mai muhimmancin gaske domin samun ingantaccen aiki tsakanin ma'aikatun gwamnati.
Shi dai aikin ginin wannan babbar sakatariyar ma'aikatan jihar an fara shi ne tun a wasu gwamnatocin jihar da suka gabata guda biyu inda a ɗauki lokaci mai tsawo ba'a kammala ba wanda hakan yasa mutane suka fara tunanin wannan aikin ba zai kammalu ba.
Tun bayan zuwan gwamnatin Kwamred Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) ya bayar da kwangilar kammala ginin tare da kuma sanya masa kayan aiki wanda yanzu aikin ya kammala.
Wannan matakin kammala aikin ginin sakatariyar yazo bayan da gwamna ya fahimci jihar Kebbi akwai ma'aikatu guda ashirin da bakwai amma ba su da isasshen wuri mai yalwa domin gudanar da ayyukan su na yau da kullum.
Haka kuma ma'aikatun suna nisa da juna wajen gudanar da ayyukan su, hakan yasa gwamna ya ƙuduri aniyar kammala wannan aikin domin ma'aikatun su kasance wuri ɗaya ta yadda za'a rage zirga-zirga mai nisa tsakanin ma'aikatun na takardu musamman masu muhimmanci da kuma samun sauƙin gudanar da aiki.
An dai fara ginin wannan babbar sakatariyar ma'aikatan jihar ne tun a shekarar 2012 a lokacin gwamnatin tsohon gwamnan Alhaji Sa'idu Usman Nasamu Dakingari inda aka fara bayar da kwangilar wurin akan kuɗi sama da Naira biliyan uku.
Daga baya aikin ya tsaya cak har gwamnatin Ɗakingari ta kammala mulkin ta ba tare da kammala aikin ba.
Bayan zuwan gwamnatin Sanata Abubakar Atiku Bagudu itama tazo ta bayar da wasu kuɗaɗe ƙalilan domin kammala aikin wanda hakan yasa aikin bai kammalu ba har itama gwamnatin ta ƙare.
Gwamnatin Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta yunkurin kammala aikin ne a karshen lokacin gwamnatin inda ta ware wasu kudaden kasa ga naira biliyan daya bayan da al'ummar jihar suka yi ta kiraye-kirayen kammala aikin.
Da haka dai har kuɗin kammala aikin ya dinga tashi har zuwa kimanin naira biliyan bakwai wanda kuma daga karshe har ya kai naira biliyan goma sha biyu.
An yi watsi da aikin tsawon lokaci ba'a kammala ba wanda hakan yasa al'ummar jihar ba tare da nuna bambancin siyasa ba su kayi ta kira da a kammala aikin domin amfanin al'ummar jihar, dama gwamnatin musamman bayan ganin irin biliyoyin kuɗi da aka kashe a wurin kuma ba'a kammala wurin ba balle a amfana da shi.
Ganin jihar ba ta da babbar sakatariyar ma'aikatan gwamnati da kuma bukatar a faɗaɗa garin shima ya taimaka wajen al'ummar jihar su yi ta kiraye-kirayen kammala aikin.
Duba da bukatar al'ummar jihar Kebbi ne yasa gwamna Kwamred Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) ya amince da tabbatar da kammala aikin da kuma fara aiki da shi inda a lokacin yaƙin neman zaɓen sa yasha alwashin kammala aikin.
Yana cin zaɓe tare da shan rantsuwar kama aiki, gwamnan ya cigaba da ƙoƙarin ganin ya cika alƙawarin sa na kammala wannan aikin.
A lokacin da ya bukaci a ba shi bayanin kuɗin da aikin zai lakume, abin mamaki sai ga shi an ce aikin zai ci kuɗi naira biliyan ashirin da daya wanda hakan yasa gwamnan ya nemi kamfanonin gida M-tech da ZBCC su gudanar da aikin inda daga karshe aka amince musu da kwangilar aikin kammala aikin.
Gwamnatin ta ɗauki matakin ne domin karfafawa kamfanonin gida kwarin guiwa wajen gudanar ingantattun ayyuka da kuma ba su dama domin bunƙasa tattalin arzikin gida.
Kamfanonin guda biyu sun bayar da adadin kuɗin kammala aikin akan naira biliyan goma inda a yanzu haka an kammala aikin inda suka gudanar da aiki mai kyau kamar yadda aka buƙata.
Kammala wannan babban aiki ya nuna ababe biyu masu muhimmanci:
1. Cika alƙawari irin na gwamna kamar yadda yayi alƙawari a lokacin yaƙin neman zaɓen sa.
2. Da kuma karfafawa kamfanonin gida wajen gogayya da manyan kamfanonin waje.
Haka kuma hakan yana nuni da cewar ya kamata al'umma su dinga zaɓen mutane nagari masu cika alƙawari.
Bisa jagoranci irin na gwamna Nasir Idris, jihar Kebbi ta ɗauki hanyar cigaba kamar sauran takwarorin ta.
No comments