Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Babban Sakataren Bayar Da Tallafin Karatu Ya Yi Kira Ga Daliban Jihar Kaduna

Hoto: shugaban majalisar matasa (NYCN) Kwamared Jibiril Salihi ne da tawagarsa suke mikawa babban Sakataren 'Kaduna State Sc...

Hoto: shugaban majalisar matasa (NYCN) Kwamared Jibiril Salihi ne da tawagarsa suke mikawa babban Sakataren 'Kaduna State Scholarship and Loans Board', Malam Hassan Rilwan sakon girmamawa yayin kammala taron a Sabon Gari Zariya.



Daga Fatima Idris Zariya

A cikin makon da ya gabata ne hukumar bayar da tallafin karatu da rance na jihar Kaduna ta shiryawa dalibai taron karawa juna sani a karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.

Wakiliyarmu na daga cikin wakilan kafafen yada labarai da suka shaida yadda taron ya gudana.

Taron an shirya shi ne da hadin guiwar majalisar matasa ta kasa reshen karamar hukumar Sabon Gari da kungiyar daliban karamar hukumar Sabon Gari duk a jihar ta Kaduna.

Taron ya sami karbuwa ta bangaren Malaman makarantu, dalibai, Sarakuna da manyan 'yan siyasar karamar hukumar Sabon Gari da jihar Kaduna baki daya.

Shugaban majalisar matasa (NYCN) na karamar hukumar Sabon Gari Kwamared Jibril Salihi ne ya fara gabatar da jawabin maraba tare da lale ga babban Sakatare a hukumar bayar da tallafin karatu na jihar Kaduna Malam Hasan Rilwan.

Bayan nan ne aka gabatar da babban Sakataren a hukumar don gabatar da bayani akan shirya taron.

Babban Sakataren ya fara ne da nuna godiya da jin dadinsa bisa yadda ya ga an karbi kiran na su hannu bibbiyu.

Da farko ya shaidawa dalibai da sauran mutanen da suka sami damar halartar taron da cewa dalilin taron shi ne don a haskawa dalibai masu neman tallafin karatu hanyar samun tallafin cikin sauki tare da kaucewa matsalar da ake samu nan da can.

Sakataren ya fara da haskawa dalibai inda ake samun matsala tun a karon farko.

Babban Sakataren ya bayyana cewa ana samun matsalar farko ne yayin fara gudanar da yin rijista a yanar Gizo da wasu ke zuwa ana yin masu, ya ce da yawa a nan ne ake tafka kurakurai dake dakile cin nasarar dalibi, inda ya kara da cewa da fatan dalibai za su yi kokarin gyara wannan tsaron don cin gajiyar.

Malam Hasan Rilwan ya kawo kididdigar yawan daliban da suka sami zuwa kasar waje karkashin tallafin da suke bayarwa a kananan hukumomi daban-daban dake fadin jihar Kaduna.

Kuma ya bayyana Karamar hukumar Sabon Gari a matsayin ta kasa wajen cin moriyar tallafin bisa rashin meman tallafin ko rashin sanin yadda ake rijistar.

Karshe ya tabbatarwa da dalibai cewa a yanzu sun fitar da tsari na musamman da ya hada kai da majalisar matasa don bayar da horo ga masu neman tallafin a matakai daban-daban karkashin Gwamnatin jihar Kaduna.

Kuma ya ce hanya a bude take don amsa duk wata tambaya ga masu neman tallafin ta yanar gizo.

Karshe ya yi godiya ga gwamnan jihar Kaduna da ya bayar da irin wannan tsarin ga dan talaka da mai kudin za su sami gajiyar tsarin. 

Honorabul Muktar Zubairu Yarima shi ya wakilci dan majalisar jiha mai wakiltar Sabon Gari. Shima a nasa sakon ya yaba ne da kokarin babban Sakataren bisa bin doka da Oda da hukumar tasa take bi kuma ya yi fatan dalibai za su gyara tsarin da suke bi a da su dauki gyaran da aka nuna  masu a wannan zama.

Shugaban majalisar matasa Kwamared Salihi ya rufe taron bayan amsa tambayoyi daban-daban da suka yiwa mahalarta taron don kaucewa matsalar da ake samu yayin gudamar da yin rijistar neman tallafin.

An yi taro lafiya an tashi lafiya. 

No comments