Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tinubu Ta Murƙushe Ƴan Ta’adda 13,000 a shekaru biyu da kafa gwamnati — Ministan Tsaro

Ministan Tsaro na Tarayya, Mohammed Badaru Abubakar, ya bayyana wasu manyan nasarori da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta c...

Ministan Tsaro na Tarayya, Mohammed Badaru Abubakar, ya bayyana wasu manyan nasarori da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta cimma a fannin tsaro cikin shekaru biyu da suka gabata. A cewarsa, gwamnatin ta gaji matsanancin ƙalubale da ya fi muni a tarihin ƙasashen yankin Sahel, amma ta samu gagarumar nasara.

Ministan ya ce, “A cikin shekaru biyu na gwamnatin Tinubu, an sami cikakken tsaro a hanyar Abuja zuwa Kaduna – wadda a baya ta kasance sananniyar hanyar masu garkuwa da mutane.”

Ya bayyana cewa daga watan Mayun 2023 zuwa yanzu, dakarun tsaro sun murƙushe fiye da ‘yan ta’adda 13,000, kuma an kawar da shugabannin Boko Haram sama da 300 a faɗin ƙasar.

“A baya idan aka ce Gambaru ko Bama, a Maiduguri, mutane kan razana saboda haɗarin hanya, amma yanzu wannan ya zama tarihi,” in ji Ministan.

A wani ɓangare na yaki da aikata laifuka a Kudu Maso Gabas, Ministan ya bayyana kama wata mota ɗauke da katan 18,000 na harsasai da fakiti 250 na wasu makamai masu haɗari, samfurin “black pellets.”

Badaru ya kuma jaddada cewa ficewar kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso daga ECOWAS ba ta yi tasiri kan tsaron iyakokin Najeriya ba, saboda ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin kare ƙasar.

“Mun ƙara haɗa kai da ma’aikatun gwamnati kamar na Man Fetur, Noma, Ruwa, Lantarki, da Ma’adanai domin tabbatar da cewa tattalin arziki da tsaro sun samu inganci,” in ji shi.

Haka zalika, dakarun Najeriya sun kama ƴan ta’adda 17,469 tare da ceto mutane 9,821 da suka sha wahala a hannun yan ta’addan. Bugu da ƙari, an gano masana’antar kera bindigogi a jihar Filato, inda aka lalata muggan makamai da dama.

Ya ƙare da cewa, ana ci gaba da ƙoƙari wajen hana matsalar tsaro yaduwa zuwa shiyyar Kudu maso Yamma ta hanyar daƙile motsin ƴan ta’adda daga yanki zuwa yanki, domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da tsaron Najeriya.

No comments