Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Buƙaci A Sako Waɗanda Aka Kama Ranar Qudus, A Biya Diyya Ga Iyalan Waɗanda Lamarin Ya Shafa

Daga Zainab Rauf Wata ƙungiya mai suna 'Concerned Abuja Indigenes' ta ƴan asalin garin Abuja ta buƙaci Shugaba Bola Ahme...

Daga Zainab Rauf

Wata ƙungiya mai suna 'Concerned Abuja Indigenes' ta ƴan asalin garin Abuja ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya bayar da umarnin sakin fiye da mutane 200 da aka kama a yayin zanga-zangar ranar Qudus ta duniya da aka yi a ranar 28 ga watan Maris a Abuja, tare da biyan diyya ga iyalan waɗanda aka kashe ko suka jikkata sakamakon abin da suka bayyana a matsayin kisan gillar sojoji.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Talata, 6 ga Mayu, mai magana da yawun ƙungiyar, Ayede Danjuma Abdul, ya ce, “Mun taru a nan yau ne a ƙarƙashin tutar adalci, haɗin kai da jin ƙai, don yin tir da Allah-wadai da tashin hankali da rashin adalcin da dakarun sojin Nijeriya suka aikata akan masu zanga-zangar ranar Qudus da kuma wasu bayin Allah ‘yan Abuja.”

Ƙungiyar ta zargi sojoji da kashe aƙalla mutane 27, da raunata fiye da 66, tare da kama sama da 380, lokacin da suka buɗe wuta kan masu zanga-zangar. “Abin da ya kamata ya kasance fitar nuna damuwa cikin lumana sai ya rikiɗe zuwa kisan gilla, inda sojoji suka fito da manyan makamai, tanka, da harsasai masu rai suka buɗe wuta akan jama’a,” in ji shi.

Ƙungiyar ta bayyana cewa wani sanannen ɗan kasuwa, Abdullahi Bello, wanda ba shi da alaƙa da wata ƙungiya ta addini, yana daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu. “An kama shi da rai, aka yi masa duka a barikin soja har ya mutu, sannan aka jefar da gawarsa a ɗakin ajiye gawa. Ba harbinsa aka yi ba – an yi masa duka ne har ya mutu,” cewar Abdul.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda aka kama sun mutu ne a hannun sojoji bayan kama su, ba a wajen zanga-zangar ba. “Waɗanda suka mutu ba dukkaninsu ne aka kashe a wajen zanga-zangar ba, wasu an kama su ne d ransu sannan aka yi musu duka har suka mutu,” in ji shi, yana mai cewa har ma da masu wucewa ta wajen zanga-zangar aka jefa cikin wannan tashin hankalin. “Wasu daga cikin 'yan asalin Abuja da ke harkokinsu na yau da kullum suma an kama su, aka yi musu dukan kawo wuƙa, wasu kuma aka kashe su.”

Ƙungiyar ta ƙara da cewa rundunar 'yan sanda ta ƙi sakin gawarwakin waɗanda aka kashe domin iyalansu su gudanar musu da jana’iza yadda ya kamata. “A ƙalla gawarwaki takwas na kwance a ɗakin ajiye gawar asibitin koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada ba tare da kula da su yadda ya kamata ba, wasu kuma suna ajiye a wasu ɗakunan ajiyar gawa huɗu daban-daban a Abuja,” in ji Abdul.

Ya kuma buƙaci Shugaba Tinubu da ya shiga tsakani. “Muna roƙon Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya bayar da umarnin sakin dukkannin gawarwakin domin gudanar musu da jana’iza kamar yadda addini ya tanada, tare da barin iyalansu su yi makoki cikin ƙima da mutunci,” in ji shi. “Fiye da mutane 200 ne ke tsare a kurkukun Kuje da Suleja, da dama kuma daga cikinsu suna fama da rauni da rashin lafiya, dole ne a ba su kulawa ta lafiya da kuma damar shari’a cikin gaggawa.”

Ƙungiyar har wala yau ta kuma buƙaci gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa game da kisan, musamman waɗanda ake zargin sun aukar da shi a cikin barikin soja. “Dole ne a hukunta dukkan sojojin da suke da hannu,” in ji Abdul. “Da dama daga cikin waɗanda aka kama ba su da alaƙa da wata ƙungiya – 'yan gari ne kawai da suka faɗa cikin wannan rikici. Dole ne a sako su nan da nan.”

Ya kuma buƙaci a biya diyya. “Gwamnati dole ne ta biya diyya ga iyalan waɗanda aka kashe, waɗanda suka ji rauni, da waɗanda harkokinsu da rayuwarsu suka lalace sakamakon wannan hari da dakarun soja suka kai.”

Yayin da suke sukar amfani da ƙarfin soja a zanga-zangar fararen hula, ƙungiyar ta ce, “Zanga-zangar farar hula ba yaƙi bane. Muna buƙatar a daina amfani da soja wajen daƙile irin waɗannan zanga-zangar.”

Abdul ya kammala da kira na haɗin kai, inda ya ce; “Wannan batu ba na ƙungiya bane ko wani. Wannan batu ya shafi kishin ƙasa ne, Haƙƙoƙin mutane, da kuma iyakokin ikon gwamnati. Mun haɗe – Musulmi da Kiristoci, ‘yan Arewa da ƴan Kudu, matasa da tsofaffi – wajen ƙin amincewa da wannan kisan gilla. Ba za mu yi shiru ba. Ba za mu ji tsoro ba. Ba za mu daina neman adalci ba.”

No comments