Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar Horas Da Hajj Da Umrah Ta Kammala Zagayen Cibiyoyin Horar Da Maniyyata A Neja

Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar Horas da Hajj da Umrah ta kammala zagayen cibiyoyin horar da maniyyata a yankunan kananan huk...

Daga Awwal Umar Kontagora

Kungiyar Horas da Hajj da Umrah ta kammala zagayen cibiyoyin horar da maniyyata a yankunan kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar Neja.

Da yake ƙarin haske ga wakilin jaridar Madogarar Labarai, jami'in yaɗa labarai na ƙungiyar, Alhaji Muhammadu Imam (PRO) ya ce sun gudanar zagayen rangadin ne don tabbatar da ayyukan horar da maniyyatan bai samu tangarda ba kamar yadda hukumar jin dadin alhazai na jihar Neja ta baiwa ƙungiyar.

Ya cigaba da cewar muna gudanar da wannan aikin tsawon shekaru ashirin zuwa yanzu, babban aikin mu shi ne horar da maniyyata yadda ake gudanar da aikin hajji a aikace, ganin hakan yasa gwamnatocin da suka gabata suke baiwa kungiyar kujeru dan raka maniyyata kasa mai tsalki dan cigaba da fadakar da su a harsunan da suke fahimta.

Imam, yace ko bayan zuwan wannan gwamnatin da ba su samu tukuicin da gwamnati ta saba baiwa kungiyar ba mu tsaya ba, kan haka hukumar jin dadin alhazai ta sanya mu cikin malamai masu ruwa da tsaki wajen wayar da kan maniyyata, shi a kowani lokaci hukumomin Saudiyya suka fitar da sabbin tsare tsaren aikin hajji da take baiwa hukumomin jin dadin alhazai na kasashen duniya, idan yazo ga hukumomin kasar nan aka baiwa hukumomin jin dadin alhazai, a jihar Neja muna yan gaba gaba wajen ganin an ba mu damar taka rawa wajen fadakar da maniyyatan jihar nan duk da cewar ba wani kaso ko daukar nauyi muke samu ba, malaman addini daga yankunan kananan hukumomi ne suke daukar nauyin cigaba da ayyukan kungiyar.

Da ya juya kan kudaden tallafi da gwamnatin tarayya ta bayar dan baiwa maniyyatan shekarar da ta gabata kuwa, ya yabawa babban manomin jiha, gwamna Umaru Mohammed Bago da sakataren hukumar Sheikh Muhammad Awwal Aliyu na ganin duk masu hakki abin ya tafi hannunsu. A cewarsa magana gaskiya jagorancin hukumar sun cancanci yabo bisa goyon bayan gwamna kan yadda suke tafiyar da ayyukan hukumar.

Alhaji Imam, ya hori maniyyatan bana da su yi taka tsantsan da guzurinsu ganin gwamnati tace kowani maniyyaci za a ba shi guzurinsa tun kafin su bar kasar nan.
Yace wannan guzurin ana bada shi dan samun biyan bukatun maniyyaci a lokacin da yake gudanar da ayyukan Ibadah a kasa mai tsalki musamman dan cin abinci da sauran zurga zurga ba tare da ya tagayyara ba. Dan haka duk maniyyacin da ya samu halin yin wannan tafiyar yayi taka tsantsan da guzurinsa dan kar ya fada tarkon barace barace ko rokon jama'a.
Da ya juya kan alkawalin gwamnati kuwa na baiwa kungiyar wasu kujerun dan samun damar rikiyar maniyyata dan cigaba da fadakar da su a kasa mai tsalki. Yace har yanzu muna bibiyar maganar, amma muna da tabbacin cewar maigirma gwamna bai manta ba, saboda tafiya da malamai yana da muhimmanci.

Gwamna ne ke da hakkin bada wadannan kujerun, kuma muna da yakini bisa abinda ya faru a shekarar da ta gabata za a cika wannan alƙawarin.

No comments