Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dalilai Uku da Suka Jawo Ziyarar Shugaba Tinubu Katsina – In ji Abdulaziz Abdulaziz

Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa na musamman kan harkokin jaridu (SSA Print Media), Malam Abdulaziz Abdulaziz, ya bayyana cewa akwai...

Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa na musamman kan harkokin jaridu (SSA Print Media), Malam Abdulaziz Abdulaziz, ya bayyana cewa akwai manyan dalilai uku da suka sanya Shugaba Bola Ahmad Tinubu kai ziyara jihar Katsina kwanan nan.

A wata hira da ya yi da Katsina Times yayin ziyararsa a ofishin jaridar ranar Lahadi, Abdulaziz ya bayyana cewa ziyarar ba wai kawai ta nuna zumunci ba ce, har ila yau, tana da alaƙa da sha’anin tsaro, ayyukan raya ƙasa, da kuma dangantakar siyasa mai zurfi da ke tsakanin shugaban da mutanen jihar Katsina.

“Na farko, batun tsaro ne. Katsina na daga cikin jihohin da matsalar 'yan bindiga ta fi kamari, kuma gwamnati na yin iya bakin ƙoƙarinta wajen shawo kan matsalar. Ziyarar Shugaba Tinubu da ganawa kai tsaye da jami’an tsaro a Katsina na nuna irin muhimmancin da gwamnati ke bai wa samar da zaman lafiya a Arewa," inji shi.

Ya kara da cewa, dalili na biyu shi ne ayyukan raya ƙasa da ake aiwatarwa a jihar. "Akwai manyan ayyuka da gwamnatin Bola Tinubu ke yi, ciki har da tituna uku da ke haɗa Katsina da wasu jihohi, wanda hakan ya nuna an sanya jihar cikin muhimman wuraren da ake mayar da hankali kansu."

Abdulaziz ya ce na uku kuma shi ne dangantakar siyasa. “Jihar Katsina gida ce a siyasance ga Shugaban Ƙasa, domin akwai alaƙa ta jini da zumunci tsakaninsa da wasu fitattun 'yan siyasa daga nan. Akwai wadanda za a iya kiran su amintattunsa, ciki har da Gwamnan jihar. Har ila yau, shugaban ya amsa gayyatar daurin auren ’yar gwamnan, inda ya halarta kuma ya sanya wa ma’auratan albarka."

Abdulaziz ya bayyana cewa dangantakar Shugaba Tinubu da jihar Katsina ta samo asali tun daga farkon siyasar sa, inda ya ce:

"Duk da cewa Tinubu ɗan Legas ne, ya fara karatun siyasa ne a hannun marigayi Janar Shehu Musa Yar’adua, wanda suka kasance tare a jam’iyyar SDP. Wannan dangantaka ce da ta ci gaba da habaka har zuwa yau.”

Ya ce hakan ne ya sanya Shugaba Tinubu bai manta da jihar Katsina ba bayan hawansa mulki, inda ya bai wa ’yan jihar dama a manyan mukamai a gwamnatinsa.

“Akwai ’yan Katsina da dama a mukamai masu mahimmanci. Misali akwai Ministan Gidaje da Ministar Ayyuka da Ƙirƙira. Haka kuma akwai shugaban hukumar NCC da wasu shugabanni na hukumomin tarayya. Wannan ya nuna yadda Shugaba Tinubu ke daraja jihar Katsina da mutanenta.”

A ƙarshe, Abdulaziz ya gode wa al’ummar jihar bisa tarba mai armashi da suka yi wa Shugaban Ƙasa da tawagarsa.

“Mun ji daɗi kwarai da gaske da irin girmamawa da karamci da al’ummar Katsina suka nuna mana. Katsina na da matuƙar muhimmanci ga wannan gwamnati. Muna roƙon Allah ya ƙara ɗorewar zumunci da haɗin kai tsakanin Shugaban Ƙasa da jama’ar jihar.” In ji shi.

No comments