Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ɗan Balki Kwamanda Ya Daina Shishshigi A Siyasar Mu - Yanga Buba

Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga mai sharhi akan harkokin siyasar Kano, Ɗan Balki Kwamanda da ya kiyaye shiga harkokin si...

Daga Awwal Umar Kontagora

An yi kira ga mai sharhi akan harkokin siyasar Kano, Ɗan Balki Kwamanda da ya kiyaye shiga harkokin siyasar Neja, domin siyasar mu ba ta dambarwa ce ba.

Jigo a jam'iyyar APC kuma ɗaya daga cikin shugabanni, Alhaji Hamza Yanga Buba, yace kalaman Dan Balki ba su dauke da komai face haddasa tunzuri da tada rigingimu, a cewarsa siyasar mu ta Neja ta bambanta da ta jihar Kano, muna da manya kuma muna da iyaye a jihar mu. Saboda kalamansa na TikTok da yake cewa gwamna Umaru Bago ya gaggauta mataimaki wannan shirme ne Dan Balki yake yi.

A jihar mu muna da manya da kananan kabilu da dama daga Gwarawa, Nupawa, Kadara, da Kambari, Ingwai, Hausawa da sauran su amma baka taba jin wata matsala a tsakanin mu. Dan haka wani daga wani gefen ba zai yi anfani da rashin tunaninsa wajen hada husuma a tsakanin mu ba.

Shin idan Umaru Bago da mataimakinsa Comr. Yakubu Garba kan su na hade wani dan tasha ne yake tsammanin zai haddasa husuma a tsakaninsu, yace yana zargin Comr. Yakubu Garba da anfani da wasu matasa dan lakadama wani matashin da yayi bidiyo akan Yakubu Garban duka. To me ya hada dan siyasar Bauchi da ke PDP da zababben shugaba daga jam'iyyar APC da ke wata jihar da har zai sa a doke shi.
Ina kira ga Dan Balki da ya sani mu siyasar mu ta Neja ba rashin hankali ba ne, ba ta rashin tarbiya ba ce. Muna siyasa ne cigaba da hadin kai dan cigaban jihar mu.
Yanga Buba, ya nemi yayan jam'iyyar APC da su hada kai su kawar da duk wani bambanci da ke tsakanin su tare da goyawa gwamnatin Umaru Bago baya musamman saboda manufofinsa manufofi ne na ciyar da jihar mu gaba.

Gwamna Umaru Bago da Comr. Yakubu Garba abu daya ne kuma manufarsu daya ce itace hadin kai da zaman lafiya da cigaban jihar mu.

Ba za mu lamunci wani daga gefe da bai san matsalolin mu ba, bai san bukatun mu ba ya rika yi mana kutse da nufin kawo rarrabuwan kawuna a jihar mu ba.

Idan Dan Balki ya taka shugabannin jiharsa ta Kano, ya taka na jihar Kaduna da Bauchi ya sha, mu a jihar Neja ba zai samu abinda yake bukata ba, dan haka ya kiyaye hawainiyarsa ta kiyayi ramar mu, muna tafiya ce bisa tsari da kyakkyawar shugabanci da kuma biyayya ga shugabannin mu.

Mu ba yan tabare ba ne, mu ba yan tasha ba ne kuma masu biyayya ne da son zaman lafiya dan cigaban jihar mu.

No comments