Daga Awwal Umar Kontagora An nemi hukumar zaben jihar Neja da ta rage kudin Fom na yan takara tare da kara wa'adin mayar da ...
Daga Awwal Umar Kontagora
An nemi hukumar zaben jihar Neja da ta rage kudin Fom na yan takara tare da kara wa'adin mayar da Fom gare ta. Dan takarar shugabancin karamar hukumar Kontagora a jam'iyyar SDP, Hon. Garba Ibrahim ne yayi kiran yammacin juma'ar da ta gabata bayan kammala mika takardunsa ga hukumar.
Hon. Garba, ya cigaba da cewar na fahimci akwai yan takarkaru da dama daga jam'iyyu da ke sha'awar takaran amma kudin da hukumar zaben ta sanya duba da yanayin da ake ciki na matsin tattalin arzikin kasa da kuma wa'adin da hukumar ta gindaya yasa jikin su yayi sanyi, akwai bukatar hukumar zabe da tayi nazari sosai dan gujewa tauye hakkin wasu.
A bayanin dan takarar, yace akwai bukatar masu kishin al'ummominsu a duk inda suke idan hukumar zabe ta bude ayyukanta na sabunta katin masu zabe da su gaggauta komawa yankunansu dan zaben mutane masu nagarta dan cigaban yankunan su da al'ummomin su.
Yana da kyau, a duk inda muke muddin da hali mu rika komawa mahaifan mu dan nuna kishi musamman a lokacin zabe.
Dan takarar yace akwai bukatar matasa da su ajiye mutuwar zuci wuri daya, su jajirce wajen bada gudunmawarsu wajen zaben mutane nagartattu da suke da ajandar gina kasa da taimakawa rayuwarsu.
Dole matasa mu ajiye zaben mutanen da aka ajiye muna, mu rika zaben mutanen da muka ajiye da kan mu, dan samar da shugabancin da zai zama mai anfani gare mu.
Idan mun cigaba da zaben mutanen da aka ajiye mana ba wanda muka ajiye da kan mu ba, za mu cigaba da zama a inda nuke ba tare da samun cigaban da muke bukata ba. Domin aikin iyayen gidan su zasu yi ba na mu ba.
Garba Ibrahim, yace muna bukatar samun jajartacciyar shugabanci mai tsari da manufa dan taimakawa wajen samun bakin zaren walwale matsalolin mu, rashin aikin yi ga matasa, inganta tsarin ilimi, tare da farfado da hanyoyin samun kudaden shigar gwamnati ta yadda za ta samu damar yin ayyukan raya kasa dan anfanin mu.
No comments