Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar CAN Ta Nemi Haɗin Gwiwar Shiga Ayyukan Hisbah

Daga Mustapha Abubakar  Madogara TV/Radio ta labarto cewa; ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) ta nemi haɗin gwiwa da kuma samu...

Daga Mustapha Abubakar 

Madogara TV/Radio ta labarto cewa; ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) ta nemi haɗin gwiwa da kuma samun cikakken damar shigar da membobinta cikin ayyukan hukumar Hisbah domin samun kyakkyawar dangantaka da haɗin kai a aiki.

Fasto Nuhu Sani, Sakataren CAN na ƙaramar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna, ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron bita na kwana ɗaya da hukumar Hisbah ta shirya a sakatariyar ƙaramar hukumar.

Fasto Sani ya ce tun da hukumar Hisbah ƙungiya ce ta addini da ke da alhakin kawar da miyagun ayyuka a cikin al’umma, ya zama dole a samu haɗin gwiwa da ƙungiyar Kiristoci domin cika wannan buri.

Sakataren ya lurantar da cewa Musulmai da Kiristoci suna zaune tare a wuri ɗaya, a don haka ya zama wajibi a daidaita ayyukan Hisbah da na Kiristoci domin samun ingantaccen sakamako.

"Mun kasance muna zaune tare a Sabon Gari, a don haka ya dace a haɗa ’yan’uwa Kiristoci cikin ayyukan Hisbah domin tabbatar da tsabtace al’umma daga ayyukan ta’asa da lalacewar tarbiyya."

"Yana da matuƙar muhimmanci la’akari da cewa ba mutanen addini guda ɗaya ke aikata laifi ba, saboda haka haɗa waɗanda ba Musulmai ba zai ƙara ƙarfin aiki da samar da kyakkyawan sakamako." In ji shi.

Tun da farko a jawabinsa, Awwal Abubakar Adam, Kwamandan hukumar Hisbah na ƙaramar hukumar Sabon Gari, ya ce suna aiki tare da dukkan hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a cikin al’umma.

Ya bayyana cewa Hisbah ta rufe fiye da rumfunan sayar da barasa har 150 da ba su da lasisi, da kuma wuraren zama da otal-otal marasa rijista inda ake kai ’yan mata masu ƙananan shekaru da matan aure domin aikata zina.

Adam ya buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki da su mara wa Hisbah baya a wannan yaƙi domin dawo da ɗabi’ar kirki a cikin al’umma.

Ya yaba da goyon bayan da gwamnatin ƙaramar hukumar ta bayar wajen amincewa da dokar da ’yan majalisa suka amince da ita wadda ta ba Hisbah doka da dama ta gudanar da aikinta.

A jawabansu daban-daban, jami’an tsaro irinsu SP Auwal Usman wanda ya wakilci ’yan sanda, RCN Musa Sunusi daga hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC), da ACM Aminu Amadu na hukumar kashe gobara ta ƙasa sun yi alƙawarin ba da goyon baya domin nasarar ayyukan Hisbah.

No comments