Daga Awwal Umar Kontagora An nemi yayan jam'iyyar APC a jihar Neja da su yi hakuri da sakamakon zaben fidda gwani dan samun ...
Daga Awwal Umar Kontagora
An nemi yayan jam'iyyar APC a jihar Neja da su yi hakuri da sakamakon zaben fidda gwani dan samun nasarar jam'iyyar a zaben kananan hukumomi mai zuwa. Wani jigo kuma dattijo a jam'iyyar, Alhaji Muhammadu Lawal Ibrahim ( Hamdala) ne yayi kiran lokacin da yake sharhi kan barazanar da wasu yayan jam'iyyar APC da zaben yan takarar shugabancin kananan hukumomi bisa cancanta bai yiwa dadi ba.
Hamdala, ya cigaba da cewar mu yan asalin CPC ne da suka yi hadin guiwa da ACN, CPC da wasu yayan jam'iyyar PDP aka kafa jam'iyyar APC, duk rawar da ake takawa a siyasa dan samun nasarar zabe mun taka shi, amma ba ai mana komai ba.
Sakamakon hakurin mu yau mun ga irin jajircewar maigirma gwamna Umaru Mohammed Bago ya ke yi na samar da ayyukan raya kasa, wanda kusan karkaru da dama da suka zama kufai sakamakon kudurce kudurcen gwamna Umaru Bago gaya yau sun fara dawowa cikin hayacin su, wanda wannan shi ne ribar dimukuradiyya da muka dade muna nema.
Dan haka, ina jawo hankalin yan siyasa musamman wadanda suka tsaya takarar fidda gwani kuma ba su samu nasara ba da su yi hakuri domin gaba yafi baya yawa, idan jam'iyyar mu ta APC ta samu nasara muna da yakinin za a cigaba da ayyukan raya kasa wanda ko ba komai tarihi zai tabbatar da irin gudunmawar da jam'iyyar APC ta bayar wajen gina kasa.
Da ya juya kan maganar kudaden da yan takarkarun suka kashe kuwa, yace ai kowa ya sani a tafiyar siyasa dole kudi yayi tasiri domin mun yi a baya na nemi shugabancin jam'iyya a yankin Neja ta arewa ban samu nasara ba kuma hakan bai sa na bar jam'iyya ba, kuma nasarorin da muke gani yau yankunan na samu da ba mu hada karfi da karfe muka marawa gwamnaati baya ba, lallai da ba mu same shi ba, hakan kuma ba zai sa in hana gwamnati ta tausaya masu ba, idan da hali su ma a janyo su kusa da gwamnati domin suna tare da jama'a kuma jama'a na tare da su hakan ya ba su kwarin guiwar tsayawa wannan takarar da ba su samu nasara ba.
Gwamnan mu adali ne kuma kwararren dan siyasa da shi mu ka yi CPC yana daga cikin wadanda suka daukaka jam'iyyar CPC a jihar nan, ina bada shawarar wadannan mutane ukun da aka tantance kuma ba su samu nasara ba, gwamnati ta janyo su kusa ta hanyar lallashi da ba su wasu damarmaki dan taya gwamnati ayyukan raya kasa.
Ina kara jaddada basu hakuri da su daina tunanin canja sheka zuwa wasu jam'iyyun, domin shi mulki na Allah ne, duk lokacin da ya zabo ka ba wani da ya isa hana ka abinda Allah ya baka, kuma idan lokaci bai yi ba sai dai mutum ya kare a tsalle tsalle, inji shi.
No comments