Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shaikh Zakzaky Ya Ƙaddamar Da Littafin Tarihinsa A Abuja

Daga Zainab Rauf, Abuja  A ranar Asabar 28 ga Shawwal 1446 (26/4/2025) aka ƙaddamar da littafin tarihin Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibr...



Daga Zainab Rauf, Abuja 

A ranar Asabar 28 ga Shawwal 1446 (26/4/2025) aka ƙaddamar da littafin tarihin Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky, wanda ya bayar da kansa mai suna “RAYUWATA”.

Ofishin Shehin Malamin ne ya wallafa hakan a ranar Lahadi a shafin Facebook da X (Twitter a da). 

A cewar bayanin, Shehin Malamin a yayin jawabinsa a wajen taron, ya bayyana cewa: “Na faɗi wani abu a taƙaice (a gabatarwan littafin), cewa, wannan littafi sakamako ne na tunani da ya zo mana da muke tsare bayan waƙi’ar da aka sanya ma suna waƙi’ar Buhari, sai muka ga Allah Ta’ala ya bar mu da rai, tunda sun zo kisa ne kawai, ba yadda za a ce ma an rayu a wannan hali, amma dai da yake Allah ne me raya wa. Kamar yadda nace, Allah da ya kai Musa (AS) hannun Fir’auna, ya raine shi, sai ya kai mu hannunsu kuma, suna so su kashe amma kuma sai suna kula da mu.

“Sai muka ga to tunda dama ta samu, bari mu faɗi wani abu wanda wataƙila in ba mu muka faɗa ba ba za a sani ba. Ita Malama sai ta yi rubutu; ita ta rubuta ne, ta saka da Ingilishi ‘A brief history of the Islamic movement.’ Ni kuma sai na yi bayani da baki, ina faɗa tana sajjalawa, muna yi kamar muna magana ne, kamar ma tana min tambayoyi ne ina amsawa, sai dai da aka rubuta littafin ba a sa tambayoyin na ta ba, sai aka mai da shi littafi. Amma kamar muna magana ne, idan mutum ya saurari sautin zai ji muna magana ne.” In ji Jagora.

Ya ƙara da cewa: “Kusan duk abin da na faɗa duk a taƙaice ne kuma a gurguje, domin kowanne ɓangare na rayuwar zai zama akwai magana mai tsawo wanda shi kansa zai iya zama littafi. Alal misali, da zan ce zan bayar da labarin karatuna na zaure ne kawai, to ai zan yi littafi ne, amma kawai sai na faɗa a gurguje kawai. Haka karatun nizamiyya, shima zai iya zama littafi, amma shima sai ya tafi a gurguje. Kuma gidajen yari kowanne littafi ne.” 

Shehin Malamin ya yi bitan wasu daga abubuwan da ya kawo a cikin littafin da suka shafi rayuwarsa da darussan da za a ɗauka. Haka kuma ya kawo wasu daga darussan da ya bayar dangane da fitintinun da suka riƙa aukuwa a cikin Harka sakamakon kusten maƙiya, inda ya ba da misalin wani rikici da ya riska bayan ya fito daga kurkukun Fatakwal karo na farko a tsakanin sistoci, da yadda ya warware shi. Da fitinar ‘yan Zuhudu da ita maƙiya suka kurɗo da ita, da fitinar Tawayiyya.”

Shehin Malamin ya ci gaba da cewa, “Maƙiya ba sun daina ba ne, an dinga kunno fitina ke nan, in sun yi na waje, sai su yi na ciki. Da yake waɗansu abubuwan duk sun ɗan fiffito a labarinmu na Tajriba da muke samu, har takai ma a wani lokaci da nake bayani nake cewa, yanzu duk wata fitina da za ta kunno kai, ana fara ta mun santa sarai. Mutum ko guna-guni ya fara yi, mukan ce ahan, dama an taɓa yi; Faqad madat sunnatil auwalin. An riga an yi irinsa.”

Ya kammala da cewa: “Amma in kace wai sai an kawar da duk matsaloli komai ya zama daidai, kowa ya zama ‘perfect’ to ai ba zai yiwu ba, kana neman ‘impossible’ ne, za ka bata lokacinka ne, a ci gaba kawai haka nan, a yi ta yi kawai har a yi nasara insha Allah.”

Kafin jawabin Jagora, sai da aka gabatar da Dr. Hussaini Hassan, wanda ya yi sharhin littafin. Bayan tsokacin Jagora, an kira ɗaiɗaikun ‘yan uwa da lajanonin Harka Islamiyyah, inda suka sayi kwafin littafan. 

A cikin mako mai kamawa za a ci gaba da ƙaddamar da littafin a Da’irorin ƙasar nan kamar yadda kwamitin ƙaddamarwar suka ba da sanarwa.

No comments