Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya zanta da manema labarai tun bayan bayyana komawar sa jam’iyyar APC daga PDP. Mujalla...
Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya zanta da manema labarai tun bayan bayyana komawar sa jam’iyyar APC daga PDP.
Mujallar ‘Politics Nigeria’ ta ruwaito cewar gwamnan Oborevwori da wasu jiga jigan jam’iyyar PDP sun bada sanarwar komawarsu APC a ƙarshen wani taro na sirri da suka gabatar a fadar gwamnatin jihar Delta.
“Zan yi muku karin haske ranar Litinin” a cewar gwamna Oborevwori ga yan jaridu bayan kammala taron.
Ya kuma kara da cewa tuni yayi wa shugabannin kananan hukumomi jihar cikakken bayanin akan matsayar da ya ɗauka, a inda ya bayyana cewa dukkanin su sun aminta su bi shi zuwa sabuwar jam’iyyar da ya koma.
“Yanzun nan na tattauna da shugabanni kanana hukumomi 25 da muke dasu akan matsayar da na ɗauka kuma dukkanin sun amince cewar suna tare da ni a wannan tafiyar.
Da dama daga cikin jiga jigan jam’iyyar PDP ne cikin su har da tsohon gwamnan jihar wanda kuma shine ɗan takarar mataimakin shugabancin kasa a zaɓen da ya gabata, Dr. Ifeanyi Okowa
No comments