Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga talakawa da matasa masu zabe da wajabtarwa kansu yin gwagwarmayar kwato kasar nan daga h...
Daga Awwal Umar Kontagora
An yi kira ga talakawa da matasa masu zabe da wajabtarwa kansu yin gwagwarmayar kwato kasar nan daga halin da aka jefa ta na rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arzikin kasa da ya jefa dubban al'umma cikin talauci. Shugaban kungiyar kare muradun talakawa ta kasa, Kwamred Imrana Wada Nas ne yayi kiran lokacin da yake tsokaci kan gwagwarmayar wasu kusoshin siyasar kasar nan wajen dunkulewa wuri daya dan ganin an kawar da mulkin jam'iyyar APC da ya bayyana haihuwar badi ba rai da ta jefa al'umma cikin halin ha'ula'i na tabarbarewar tsaro, matsin tattalin arziki da karuwar talauci.
Shugaban ya cigaba da cewar yin gwagwarmayar kwatar yanci wajibi ne, domin dole ne matasa da talakawa da ake anfani da su wajen yakin neman zabe idan an samu nasara a yi watsi da su da su tashi tsaye wajen fadakar da junan su hanyoyin da zasu bi wanda bai sabawa dokokin kasa ba wajen ceto kasar su da kubutar da ita hannun yan fushi da fushin wani wadanda ba su da wani kudurin da ya wuce su zama shugabanni koda ba su da kwarewar da zasu yi anfani da wajen inganta rayuwar al'umma tare da tabbatar da kasar a matsayin kasa daya, al'umma daya.
Tarihi ya nuna mana irin namijin kokarin da su marigayi Sir. Tafawa Balewa, Ahmad Bello Sardaunan sokoto su kayi na tsayin daka wajen ganin kasar nan ta tsaya da kafarta, amma aka yi anfani da wasu gubatattu aka salwantar da rayukan su, saboda mummunar manufar wasu akan kasar.
Bayan wafatinsu, sun bar wasici ga mutanen da suke ganin na kirki ne, amma saboda tsoron kamu ko dauri, ko tsoron wani barazana saboda wasu abubuwan da aka aiwatar karkashin su yau suna raye amma ba sa iya tsawatarwa, dole mu fadawa kan mu gaskiya, dan saukin da muke samu na mummunar manufar da ke boye, inuwar wadannan ne da muke gani ba komai ba, yasa wasu abubuwan ko an bullo da su ba sa tasiri.
Wada Nas, yace yau mun fito muna bin sauran wadannan gurabun muna tunatar da su, cewar su sani ba haka suka gaji kasar nan ba, wajibin su ne su fito su tsaya tsayin daka wajen ganin an dawo da abubuwan kan bagiren su, in ba haka ba nan gaba, masu tasowa zasu yi yunkurin da ba za a iya tausa su ba.
Matashin, yace abin kunya da bakin ciki, shugabannin da muke kyautata za su iya tsare mutuncin kasar sun koma wajen gasar tarawa yayansu da jikokinsu dukiyoyi alhalin kasar a kullun kara nutsewa ta ke, wanda hakan babban kuskure ne.
A zaben 2013 wasu sun yi yunkuri na hadewa dan kafa jam'iyyar da za ta kawar da gwamnatin PDP, a tunaninsu jam'iyyar PDP ce ta jefa kasar a wannan halin, amma bayan samun nasarar kawar da PDP din, aka bada kasar ga mutumin da ake kyautata zaton da gaske yake, sai ya zama shekaru takwas din sa akan karagar mulki ba abinda ya wakana face karuwar tabarbarewa da lalacewar kasar sakamakon karuwar rashin tsaro, da rashin sanin makaman mulki. Yau bayan tafiyar gwamnatinsa, muna tsammanin shugaban da ke mulkar kasar a yanzu zai yi katabus wajen kawo sauye sauyen da zasu kawo gyara, mai makon gyara sai abin a kullun kara tsamari yake, ta yadda duk da kudaden shigar da ake ikirarin karuwarsa, talakawa al'ummar kasa sun samu kan su a yanayin da ba zai kwatantu ba saboda munin shi.
Ba mu ce a bar jam'iyya ba, abinda muke fadawa matasan mu shi ne, mu ajiye kwadayi da tsoron talauci ko dauri mu tabbatar mun tsayu wajen tabbatar da dawo da martabar mu da martabar kasar mu wajen yaki da matsalar tsaro, dawo da martabar tattalin arzikin kasar dan ganin mun ceto kasar nan daga wadannan yan jari hujjar.
Duk dan siyasar da ya baka kudi ka karba, daman kudin mu ne amma mu yi abinda ya dace a lokacin zabe wajen zaben mutane nagartattu da muke da yakinin sun san abinda ya dace koda ba yan jam'iyyar mu ba ne, amma idan mun duba duk cikin jam'iyyun kasar nan, ba jam'iyyar da ke da tsari da sanin makamar aiki kamar jam'iyyar PDP.
Yau za ka ga shugaba, yana da kamfanoni sama da goma mallakinsa, duk wani aikin da gwamnati za ta gudanar kamfaninsa yake baiwa, shi ya assasa karuwar kungiyoyin ta'addanci dan dauke hankalin jama'a akan abinda ya dace, sabanin a baya da ake watsa ayyuka ga jama'a ta yadda ake samun walwala da yin gaba da rashin aikin yi ga matasa tare da ganin talauci bai samu gindin zama ba.
Kwamred Imrana, ya cigaba da cewar mun fito ne dan fadakar da masu ruwa da tsaki musamman a arewa cewar tura fa ta kai bango, dole su fito su tsawatar tare da ganin an dawo bisa turbar da ta dace, amma bai kamata su zura ido wannan mummunan halin na cigaba da wanzuwa ba, yau matasa mune kashin bayar kafuwar kowace gwamnati amma mu ne a baya saboda rashin shugabanci na gari.
Idan muka duba, duk wani gurbi na gwamnati ko shugabanci yayan su suke kokarin su gaje su, to menene matsayin yayan talakawa da suka rana da iska wajen kafa gwamnatin, ina matsayin matasan mu masu kwazo da ilimi wadanda suka ma samu damar yin karatun, ko a haka ake tsammanin za a cigaba. Ko kuwa an ki magance matsalar tsaro da tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan ne saboda manufarsu ta boye na cigaba da bautar da yayan talakawa, ya kamata mu farka.
Wannan aikin yanzu muka fara shi, kuma da yardar Allah duk wani barazana ba zai sa mu fasa ba, saboda hakkin mu ne mu tashi tsaye wajen ceto kasar mu ta haihuwa, wadda ban da Nijeriya ba mu da wata kasar da muke tinkaho da ita dole ne mu hada karfi da karfe sannan mu hada kai a manufa daya na ceto kasar nan da yankin arewacin kasar nan.
A shekarun baya ba mu san fashi da makami ba, ba mu san garkuwa da mutane, kai duk wani aikin assha bai da gindin zama a arewa sai dai mu gani a talabijin ko a labarai, amma yau mun wayi gari muna kallon shi a gidajen mu, an kassara karkarun mu, an kassara yan uwan mu wanda hakan yayi tasiri ne wajen kawar da tunanin al'umma dan samun damar aiwatar da mummunar nufinsu ga kasar nan.
No comments