Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jigon APC ya yabawa Gwamna Bago kan aikin hanyar Kontagora-Rijau

Daga Awwal Umar Kontagora Wani jigo a jam'iyyar APC tsohon mamba a hukumar jin dadin alhazai ta jihar Neja, Alhaji Muhammadu...

Daga Awwal Umar Kontagora

Wani jigo a jam'iyyar APC tsohon mamba a hukumar jin dadin alhazai ta jihar Neja, Alhaji Muhammadu Lawal Ibrahim ( Hamdala) ya yabawa gwamna Umar Mohammed Bago kan yunkurinsa na sharewa al'ummomin kananan hukumomin Kontagora da Mariga zuwa karamar hukumar Rijau kan matsalar aikin hanyar da ya shafe shekaru talatin suna nema.

Lawal Hamdala, ya cigaba da cewar bayan dawowar mu minna da zama wanda aka tilasta mana yin gudun hijira muna kudurin komawa garuruwan mu na haihuwa amma saboda lalacewar hanyar ta tilasta mana zaman dirshen ba tare da yunkurin komawar mu garuruwan mu na haihuwa, mun yi daga jijiyar wuya da tare da neman alfarma ga gwamnatocin da suka shude amma ba a saurare mu ba duk da cewar al'ummomin suna bada kuri'a a lokacin zabe fiye da wasu yankunan.

Amma bayan samun nasarar zaben fidda gwani kafin babban zaben da ya gabata, gwamna Umar Bago ya sha alwashin kammala aikin hanyar Rijau zuwa Kontagora, wanda hakan ya nuna cewar gwamna mai kishi ne da son cigaban jihar Neja, tare da tabbatar da kudurinsa ga bunkasa tattalin arzikin jihar.

Lawal Hamdala, ya bayyana hakan ne a yammacin littinin din makon nan lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan wani rangadin gani da ido da wasu yan jarida ke yi dan ganewa idanunsu ayyukan raya kasa da gwamnan ya sanya a gaba.

Hamdala, yace ku yan kasa ne kuma kuna sane da halin da al'ummomin karkara ke fama da shi, musamman kananan hukumomin da ke iyakokin jihar Neja da wasu jahohin na lalacewar hanya da matsalolin tsaro, amma yau kun ga yadda aikin hanyar da ba ta wuce tafiyar minti arba'in da biyar zuwa awa daya take daukar matafiya sama da awanni biyar zuwa shida ta kowace gefe ke cigaba ba bayan zuwan wannan gwamnatin ta babban manomin jiha, Dakta Umar Mohammed Bago.

Hakan, na nuna da gaske yi wajen yunkurin dawo da martabar noma, bunkasa kananan sana'o'i da dubaru samar da bakin zaren shawo kan matsalar tsaro a jihar nan.

Dan haka, ina baiwa al'ummomin mu musamman na yankunan karkarun da suka hada Mariga, Kontagora da Rijau da mu cigaba da baiwa gwamnatin jiha goyon baya, da kyawawan addu'o'in samun nasara. Wannan aikin yafi shekaru sittin muna bukatar shi, amma zafafawa kuwa ya kai shekaru talatin muna yi ta hanyar kiraye kiraye da neman alfarma amma sai a wannan gwamnatin ne muke ganin hakar mu za ta cin ma ruwa.

Alhaji Lawal, yace masu korafin cewar gwamnati ta ciwo bashi ne take wannan aikin, to ina son masu irin wannan tunanin su sani ba wata gwamnatin da ta shude a jihar nan da ba ta ciwo bashi ba, amma ba gwamnatin da ta ciwo bashi kuma tayi anfani da kudaden bashin inda ya dace sai gwamnatin Umaru Bago.

Saboda haka muna jaddada goyon bayan mu gare shi akan kudurin samar da sabuwar jihar Neja, wanda irin wadannan matsalolin idan gwamnati ta iya shawo kan su zai kawo karshen matsalar durkushewar kasuwanni karkaru da ke samar da kudaden shiga ga kananan hukumomi, da kuma dawo da martabar karkaru na yin gudun hijira zuwa marayu saboda matsalolin rayuwa da suke fuskanta.

Dan siyasar, ya jawo hankalin kamfanonin da aka baiwa ayyukan hanyoyin da su ji tsoron Allah su sanya kishin kasa wajen gudanar da ayyuka masu inganci kamar yadda suka yi alkwali.

No comments