Daga Idris Ibrahim, Azare Wata mummunar gobara ta tashi a kasuwar yan gwanjo ta Terminus dake garin Jos a Taraiyar Nijeriya. Go...
Daga Idris Ibrahim, Azare
Wata mummunar gobara ta tashi a kasuwar yan gwanjo ta Terminus dake garin Jos a Taraiyar Nijeriya.
Gobarar wacce aka ce ta tashi cikin daren juya Talata 29/4/2025 wadda kuma har waye war garin yau Laraba tana ci.
Ana zargin wutar ta ta shi me kusa da mai cajin waya kamar yadda wani ganau ya sahaidawa wakilinmu.
An ɗauki tsawon lokaci ana ƙoƙarin kashe wutar amma ta gagari mutanen da suka kawo ɗauki.
Wani da ya je wajen ya shaida wa wakilinmu yadda wutar ta yi ɓarna a 'yan Gwanjon ba a cewa komai.
Ya ce babbar matsalar da ake samu shi ne rashin samun motocin kashe gobara a kasuwanni.
Ya ƙara da cewa da motocin kashe gobarar da wannan wutar ba ta yi wannan ɓarnar haka ba. Mota ɗaya ce ta iya zuwa wannan wajen, in ji shi.
A ƙarshe ya yi kira ga hukumomi da su samar da ma'aikatan kashe gobara a kasuwanni kuma a tanadar musu da kayan aiki.
No comments