Wannan takardar roÆ™o ne ko nace koke daga al’ummar garin Kamagata dake Æ™aramar Hukumar Dawakin Kudu. Mai girma Gwamna sunana Abu...
Wannan takardar roÆ™o ne ko nace koke daga al’ummar garin Kamagata dake Æ™aramar Hukumar Dawakin Kudu.
Mai girma Gwamna sunana Abubakar Hamisu Kamagata kuma Digachin Kamagata dake ƙaramar hukumar Dawakin Kudu. Gari ne dake ɗauke da dimbin al'umma kuma kashi 90% matasa ne.
Kamar yadda mai girma gwamna zai gani a jikin wannan rubutu akwai hotuna, waɗannan hotunan ba komai bane face makarantar firamare ta gari na wacce za ka ga lalacewar da ta yi a ɗaya gefen kuma wani gini ne da ba a kammala ba da mutanen gari masu taro da sisi muka haɗa muka fara ginawa amma ƙarasawa ta gagara.
A madadina da na dukkan wani mutum dake garina muna neman ɗaukin bulo a makarantar firamaren da kuma makarantar ƙaramar Sakandaren ɗinmu domin bulo ɗin da suke tsaye yanzun duk shekara sai ya zama kamar haka mu haɗa kuɗi mu gyara amma ya yi lalacewar da indai damina ta zo sai ya koma gidan jiya.
Da fatan kokenmu zai isa inda ya dace.
Muna godiya.
No comments