Hukumar Raya Ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP) ta yaba wa Gwamna Dauda Lawal bisa jajircewarsa wajen ba da tallafin da z...
Hukumar Raya Ƙasashe ta Majalisar ÆŠinkin Duniya (UNDP) ta yaba wa Gwamna Dauda Lawal bisa jajircewarsa wajen ba da tallafin da zai amfani al’ummar jihar Zamfara.
A ranar Laraba ne hukumar UNDP ta ƙaddamar da Cibiyar Magance Ƙalubalen Ci Gaba a Yankin Arewa maso Yamma 'Northwest Prevention Facility Project' a ɗakin taro na Garba Nadama da ke sakatariyar jihar, Gusau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa aikin ya haÉ—a da raba kayan noman rani ga manoma 300 da aka zabo bisa la’akari da buÆ™atunsu.
Sanarwar ta Æ™ara da cewa, ’yan kasuwa 1,000 za su samu jarin fara aiki na Naira 150,000 kowannensu, da nufin sauya akalar kasuwancin su zuwa sana’o’i na zamani a faÉ—in Jihar Zamfara.
A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa bayan hawansa mulki, gwamnatinsa ta bullo da shirye-shiryen ƙarfafawa da dama tare da samar da damarmaki don cimma manufofinsa na ceto.
“WaÉ—annan tsare-tsare ba wani kebantaccen abu ba ne, wani É“angare ne na babban burinmu wajen samar da jihar Zamfara mai albarka don haÉ—a abokan hulÉ—a don magance É—imbim matsalolin zamantakewa da tattalin arziki.
“Yawancin tsare-tsare na rage raÉ—aÉ—in talauci da wannan gwamnati ta bullo da su sun yi tasiri ga rayuwar dubban ‘yan jihar, Æ™udirin gwamnatinmu na kawar da raÉ—aÉ—in talauci yana haifar da É—a mai ido. Za mu ci gaba da yin haÉ—in gwiwa tare da UNDP da sauran Æ™ungiyoyin masu ba da tallafi don samar da É—orewar hanyoyi don fitar da mutanenmu daga Æ™angin talauci.
“Tun da aka fara wannan shirin na bayyana cewa akwai tsari wajen zabi na gaskiya na waÉ—anda za su ci gajiyar shirin, don haka an zabo waÉ—anda suka amfana daga garuruwa da Æ™auyuka kamar Sankalawa, Furfuri, Karal, Gusau, da Bungudu.
“Ina yawan nanata cewa Æ™arfafa tattalin arziki dole ne ya kasance cikin haÉ—in kai a Æ™arÆ™ashin mu, ba tare da barin al’umma a baya ba, shi ya
No comments