Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zaɓen 2027: Shugaba Tinubu na shirin yi wa gwamnonin PDP ɗauki ɗaya-ɗaya

Daga Zainab Rauf, Abuja A yayin da ake ci gaba da tattara ƙarfi da ƙwanji a wuri guda domin tunkarar zaɓen 2027, wata majiya ta ...

Daga Zainab Rauf, Abuja

A yayin da ake ci gaba da tattara ƙarfi da ƙwanji a wuri guda domin tunkarar zaɓen 2027, wata majiya ta shaidawa Madogara TV/Radio cewa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu na shirin gamsar da gwamnonin PDP domin marawa neman takararsa a wa'adi na biyu baya. 

Majiyar ta ce shugaban yana ci gaba da bibiyar gwamnonin domin ganin ya cimma gaci a zaɓen 2027. 

Idan ba ku manta ba, a yau ne gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya ayyana canza sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC. 

Kazalika tsohon gwamnan jihar Delta kuma abokin takarar Atiku Abubakar na PDP a zaɓen 2023, Ifeanyi Okowa ya fice daga jam'iyyar PDP tare da sanar da komawarsa APC. 

A mako mai zuwa ne ake sa ranza a yi bikin karɓansu a jam'iyyar tare da ilahirin magoya bayansu waɗanda su ka haɗa da kwamishoni da shuwagabannin ƙananan hukumomin jihar da dai sauransu.

Duk da ayyana tawaye ga jam'iyyar APC da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-rufai ya yi zuwa SDP, har yanzu babu wani mai muƙami mai ci da ya bi sa cikin jam'iyyar sai dai tsofaffin masu muƙami da aka fusata a jam'iyyar PDP ko APC.

No comments