Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE
Monday, June 2

Pages

Labarai:

Matasan Arewa Sun Mara Wa Tikitin Makinde-Bala Mohammed Goyon Baya Don Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 2027

Daga Zainab Rauf

Ƙungiyar ci gaban matasan Arewa ta 'Arewa Youth Alliance for Progress (AYAP)' ta buƙaci a ayyana tikitin takarar shugabancin ƙasa na haɗin gwiwa tsakanin Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed (Kauran Bauchi) a gabanin zaɓen shekarar 2027 a Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Juma'a, ƙungiyar ta ce ta yanke wannan shawara ne bayan “tattaunawa da tunani mai zurfi” dangane da taɓarɓarewar matsalolin tattalin arziƙi da tsaro a ƙarƙashin gwamnatin yanzu. 

“Yanzu Nijeriya na fuskantar wani muhimmin lokaci a tarihin ta,” in ji AYAP. “Abin takaici, gwamnatin yanzu ta gaza cika manyan alƙawuran da ta ɗauka na farfaɗo da tattalin arziƙi da tabbatar da tsaro.”

Ƙungiyar ta nuna damuwa kan “tsananin matsin tattalin arziƙi, hauhawar farashi fiye da ƙima, ƙarancin ayyukan yi, da ƙaruwar talauci,” tana zargin gwamnatin tarayya da bin manufofi marasa tsari da hangen nesa, waɗanda ba su san halin da talakawan Nijeriya ke ciki ba.

AYAP ta kuma koka da ci gaba da taɓarɓarewar tsaro da ke addabar sassa daban-daban na ƙasar. “Daga ta’addanci a Arewa, sace mutane a tsakiyar Nijeriya, zuwa aikata manyan laifuka a Kudu, gwamnatin tarayya ta nuna gazawa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a,” in ji su.

Ƙungiyar matasan ta buƙaci haɗin gwiwa tsakanin Kudu da Arewa domin “warkar da ƙasa da sake gina ta,” tana jaddada cewa Injiniya Seyi Makinde da Sanata Bala Mohammed suna da hangen nesa, ƙwarewa, da karɓuwa a ƙasa baki ɗaya da ake buƙata don haɗe Nijeriya da kai ta tudun mun tsira.

“Ya zama dole a fahimci cewa dole ne Kudu ta kammala wa'adin mulkinta na shekaru takwas domin adalci su tabbata,” in ji ƙungiyar, tana mai jaddada cewa adalci da daidaito suna buƙatar a bar mulki a hannun Kudun Nijeriya a 2027.

Ta yaba da “ƙwarewar aiki, gaskiya, da hangen nesa” na Makinde da kuma “kishin ƙasa da jagorancin kasa” na Bala Mohammed, inda ta buƙaci 'yan Nijeriya, ƙungiyoyin matasa, ƙungiyoyin mata, ƙungiyoyin fararen hula, da 'yan siyasa masu kishin ƙasa su mara wa wannan tikitin baya.

“Nijeriya ta cancanci fiye da haka. Nijeriya na iya samun ci gaba. Lokaci ya yi da za a dawo da mafarkin da iyayenmu na kafa ƙasa suka yi,” sanarwar da Zakariyyah Abubakar, mai tsara taro na AYAP, ya sanya wa hannu ta jaddada.

No comments