Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gidauniyar Alfur'qan Ta Gina Masallacin Juma'a Irinsa Na Farko A Minna

Da Awwal Umar Kontagora Gidauniyar Alfur'qan ta gina masallacin Juma'a irinsa na farko a Minna inda ta miƙa jagorancin m...

Da Awwal Umar Kontagora

Gidauniyar Alfur'qan ta gina masallacin Juma'a irinsa na farko a Minna inda ta miƙa jagorancin masallacin ga Ƙungiyar JIBWIS ta kasa reshen jihar Neja.

Tunda farko a bayanin babban daraktan ɓangaren kula da harkokin ilimi da fadakarwa, Sheikh Muhammad Ashir Abubakar, ya ce wannan gidauniyar ta dauki tsawon shekaru talatin tana yi wa addinin musulunci hidima a kasar nan, inda bayan horarwa da ilmantar da malamai yadda ake gudanar da limanci sannan ta watsa su cikin kasa dan yiwa addinin musulunci, ta gina masallatan juma'ada dama da kuma bada tallafi ga masu rauni musamman ciyarwa lokacin watan Ramadan da makamantansu.

Ya ce akwai wurare da dama da suke gina masallatai kuma su jagorance su, amma wannan babban masallacin juma'ar da aka gina a garin minna fadar babban birnin jihar Neja an mika jagorancin shi ne ga kungiyar JIBWIS wadanda bayan gwamnatin jihar ta baiwa filin dan gina masallacin juma'a ta nemi tallafin gidauniyar Alfur'qan don gina wannan masallacin.

A bayaninsa, shugaban ƙungiyar ta jihar Neja, Alhaji Hassan Nuhu (Mayanan Minna) ya yabawa gidauniyar Alfur'qan kan wannan namijin aikin da tayi addinin musulunci.

Mayanan Minna, ya cigaba da cewar zuwa yanzu an nada limamai guda biyu, nan gaba za a bada sunan limami na uku, wadanda aka nadan sun hada da Sheikh Aliyu Muhammad Sani Adarawa a matsayin limami na farko, sai Malam Abubakar Umar a matsayin na'ibinsa.
Yace, akwai tsare tsaren da muke fatar nan gaba jagororin wannan masallacin zasu fitar da ya hada kafa kwalejin sanin makaman aikin akan bincike da lissafi ta yadda za a samar da hanyoyin kudaden shiga wajen rage neman taimako akan wasu harkokin addini saboda samun hanyoyin kudaden shiga.

A bayanin shugaban kungiyar ta kasa, Sheikh Bala Lau, a tabakin wakilinsa, ya yabawa gidauniyar Alfur'qan bisa kammala aikin wannan masallacin kan kari.
Bala Lau, ya jawo hankalin jagororin wannan masallacin da su kirkiro wasu muhimman abubuwa dan raya wannan masallacin, ba sallar juma'a kadai ba, ya zama cibiya na yada harkokin addini wanda zai taimaka wajen yada ilimi na addinin musulunci.

A ta'alikin limamin da ya jagoranci sallar juma'ar, Sheikh Imam Aminu Ahmad Alfur'qan, ya jawo hankalin al'ummar musulmi muhimmancin kwanaki goma na Zul-Hajj.

Ya bayyana cewar wadannan kwanaki akwai alherai da falala a cikinsu musamman ranar Arfa.

Haka kuma, ya nemi masu hannu da shuni dama wadanda suke da hali da su fitar da duniyoyinsu wajen tallafawa al'umma dan samun yin sallah cikin wadata, musamman ganin halin kuncin rayuwa da fatara da ya yiwa al'umma katutu.

Limamin ya yi addu'o'in samun zaman lafiya ga kasa musamman jahohin da iftila'in Boko Haram, Garkuwa da mutane yaiwa tutsu.

Haka, ya nemi jama'a da su ji tsoron Allah su rika yiwa kawunan su hisabi, wajen daina ayyukan sabo, da ya shafi zinace zinace, zubar da jinin bayin Allah, satar duniyar gwamnati da kuma nuna soyayya da kaunar juna a tsakanin su.

Masallacin dai an kashe sama da naira mikiyan dari biyu wajen gina shi. An gina masallacin ne daura da rukunin three arm-zone da ke unguwar Maitumbi cikin karamar hukumar Chanchaga.

Ko a yan shekarun da suka gabata cibiyar ta Alfur'qan tana masallacin juma'a a cikin garin Paiko da ke karamar hukumar Paikoro ta jihar Neja da karin wani masallacin a cikin garin Paikon.

No comments