Dandalin ƴan jaridar yanar gizo ta Zariya wacce aka fi sani da 'Zaria Online Journalists Forum' ta bayyana matuƙar alhin...
Dandalin ƴan jaridar yanar gizo ta Zariya wacce aka fi sani da 'Zaria Online Journalists Forum' ta bayyana matuƙar alhininta kan rasuwar shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai ta Nijeriya (MOPPAN), Malam Maikudi Umar, wanda aka fi sani da Cashman.
A cewar wata sanarwa da Mataimakin Shugaban Dandalin, Idris Umar, ya sanya wa hannu, gogaggen mai shirya fina-finan kuma malamin makaranta ya rasu ne a daren Laraba bayan fama da doguwar jinya. Ya rasu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya, yana da shekara 62 a duniya.
Malam Maikudi Umar fitaccen ɗan fim ne a Nijeriya, wanda ake girmamawa sosai saboda rawar da ya taka a masana’antar Kannywood da kuma Nollywood. An san shi a matsayin ɗan wasa, mai shirya fina-finai, kuma darakta mai kishin sana’arsa, wanda ayyukansa suka taka rawar gani wajen inganta masana’antar fina-finai a ƙasar nan.
Baya ga harkar fim, Umar ya kasance babban malami kuma jairtacce a Kwalejin Nuhu Bamalli da ke Zariya. Za a tuna da shi a matsayin jagora mai ba da horo ga ɗalibai da matasa masu sha’awar aikin ƙirƙire-ƙirƙire.
An gudanar da jana’izarsa a ranar Alhamis a makabartar Dembo da ke Zariya, bisa tanadin musulunci. Taron jana’izar ya samun halartar ɗimbin al'umma ciki har da manyan mutane, abokai da abokan aikinsa daga masana’antar fim.
“A madadin dukkan ‘yan jarida na yanar gizo da ke Zariya, muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalansa, abokansa, abokan aikinsa, ɗalibansa, da kuma al’ummar Kannywood da Nollywood baki ɗaya,” in ji sanarwar.
“Za a ci gaba da tuna Malam Maikudi Umar (Cashman) a matsayin mutum mai ƙwarewa da ya riƙa bayar da labaran ƙwarewa tare da horarwa. Muna addu'ar Allah ya jikansa da rahama kuma ya bai wa dukkan waɗanda ya bari haƙuri da juriya,” sanarwar ta ƙarƙare.
No comments