Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

IPAC Ta Goyi Bayan Hukumar Zabe Don Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomin Jihar Neja

Daga Awwal Umar Kontagora Hadaddiyar kungiyar siyasun Nijeriya (Inter-Party Advisory Council Of Nigeria) ta bayyana goyon bayanta ga hukumar...



Daga Awwal Umar Kontagora

Hadaddiyar kungiyar siyasun Nijeriya (Inter-Party Advisory Council Of Nigeria) ta bayyana goyon bayanta ga hukumar zabe na jihar Neja da gudanar da zabukan kananan hukumomin jihar ranar daya ga watan Nuwambar shekarar 2025.

Shugaban kungiyar a jihar Neja, Hon. Mohammed Bello Maikujeri ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da kungiyar ta kira ranar asabar din makon nan a sakatariyar kungiyar da ke minna.

Bello Maikujeri, ya cigaba da cewar hukumar zabe (NSIEC) ta kirkiro sabbin tsare tsare wanda babu su a baya na tabbatar da kowace jam'iyya a sada ta da duk wani abinda hukumar za ta aiwatar da tattaunawa, bayan nan an kirkiro bangaren shari'a, wanda duk jam'iyyar da ke da korafi za ta gabatar da korafin ta ga sashen bisa dokokin zabe na jihar Neja.

Yace hukumar ta gabatar da jadawalin zabe tun ranar shida ga watan Maris na wannan shekarar, wanda in ka duba a baya ana gudanar da zabukan ne cikin watanni uku, amma sakamakon sabin tsare tsaren hukumar da majalisar dokoki ta yiwa gyaran fuska za a rika gabatar fara shirye shirye zuwa zabe cikin watanni shida.

Wanda dan takarar shugabancin karamar hukuma da mataimakinsa zasu biya kudaden gudanar da aiki naira dubu dari uku, yayin da dan takarar kansula zai biya naira dubu dari.

Yace daga cikin jam'iyyu goma sha tara da ake da su a jihar, jam'iyya goma ne suka cika sharuddan shiga zabe zuwa yanzu.

Maikujeri, yace sakamakon takaddamar da ke tsakanin jam'iyyar NNPP a jihar, bangaren kayan marmari ne suke da shaida hannun hukumar zabe. Yace bisa ka'ida, idan jam'iyya ta canja tambari ko shugabanci wajibi ne ta sanar da hukumar zabe amma a jihar Neja jam'iyyar NNPP ba tai hakan ba.
Saboda haka, rikicin da ke tsakanin shugabancin NNPP ba abu ne da ya shafi kungiyar IPAC ba, domin ba a shugabancin jam'iyya da bangarori biyu, wajibi jam'iyya ta sanar da duk wani tsare tsaren ta ga hukumomin da abin ya shafa ga hukumomin da abin ya shafa tun gabanin tunkarar zabe, dan haka NNPP na cikin jam'iyyu tara da ba zasu shiga wannan zaben kananan hukumomin ba, sakamakon rashin dunke barakar da tsakanin yayan ta.

Kungiyar ta taya gwamna Umar Mohammed Bago murnar cika shekaru biyu kan karagar mulkin jihar.
A takardar manema labarai da IPAC ta gabatar mai dauke da sanya hannun shugaban kungiyar da sakatarenta, Hon. Mohammed Bello Maikujeri da Aliyu Muhammad, ta yabawa gwamnatin jihar Neja, bisa jagorancin babban manomin jiha, Dakta Umaru Mohammed Bago na gabatar da ayyukan cigaban kasa a jihar wanda a tarihin siyasa ba a taba gabatar da irinsu a jihar cikin shekaru biyu ba.

Kungiyar ta jawo hankalin gwamnatin jiha wajen mayar da hankalin kan matsalolin tsaro da kare rayukan al'ummar jihar, takardar tace matsalar tsaro a halin yanzu a kasar nan ya zama ruwan dare wanda ya haifar da ta'addanci, garkuwa da mutane, rikicin manoma da makiyaya da makamantan su. Wadannan matsalolin su suka haifar talauci, rashin aikin yi da kuma karuwar rashawa, akwai bukatar a dauki tsauraran matakai da suka dace.

Dan samun damar kyakkyawar fahimta ga al'ummar kasa, inganta tsarin ilimi da samar da gurabun ayyuka, kawar da rashawa dan samun ingantacciyar gwamnati da samar da kafar tattaunawa dan walwale dukkanin wata takaddama tsakanin al'umma.

Takardar tace a bangaren siyasa kuwa, IPAC tana da kyakkyawar fahimta da gwamnati ta hannun mai baiwa gwamna shawara akan harkokin siyasa da tsare tsare da dukkanin sauran jam'iyyun siyasa a jihar nan. Kungiyar kuma ta jajanwa al'ummar karamar hukumar Mokwa kan iftila'in ambaliyar ruwa da yayi sanadin rasa rayukan al'umma da dama da dukiyoyi. Kuma ta jawo hankalin gwamnati da ta dauki dukkanin matakan da suka dace wajen kare sauran bangarora dan samar masu ingantacciyar rayuwa na nan gaba.

No comments