Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

AGAFPAMA Da MOURE Consult Za Su Bai Wa Manoma Dubu Tallafin Kayan Noma Cikin Farashi Mai Sauki A Neja

Daga Awwal Umar Kontagora Hadaddiyar kungiyar manoma (All Green Agro Field Farmers Processors and marketers Association) wato AGAFPAMA a tak...


Daga Awwal Umar Kontagora

Hadaddiyar kungiyar manoma (All Green Agro Field Farmers Processors and marketers Association) wato AGAFPAMA a takaice tare da hadin guiwar kamfanin MOURE Consult za su baiwa manoma dubu goma tallafin kayan noma cikin saukin farashi a jihar Neja.

A bayanin shugaban kungiyar ta jihar Neja kuma sakataren kungiyar ta kasa, Amb. Dr. Nura Hashim (Tallafin Bosso Karami) ya bayyana cewar sakamakon matsayar gwamnatin tarayya na sawo abinci, bayan a shekarar da ta gabata manoma sun saye kayan noma da tsada, kuma gwamnatin ba tai la'akari da hasarar da ta janyowa manoma ba, yasa kungiyar yin hubbasa wajen hadin guiwa da kamfanoni masu zaman kan su wajen sayo kayan aikin goma da ya shafi taki, da maganin feshi da iraruwa dan sayarwa manoma cikin saukin farashi, inda manoman zasu biya kashi arba'in lakadan bayan cire anfanin goma kuma su biya sauran kashi sittin na abinda aka ba su.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da shirin raba kayan ga manoman da suka cika ka'idar da aka gindaya.

An dai gudanar da taron kaddamarwar ne a harabar fadar hakimin Bosso, Alhaji Mu'azu Adamu Laka da ke karamar hukumar Bosso ranar asabar din makon nan.

Tallafin na Bosso, ya cigaba da cewar dukkanin manomin da ya samu wannan kayan, mun tabbatar ya cika ka'idar da muka gindaya masa na biyan sauran kashi sittin bayan cire anfanin gona. Ba mu tsaya nan ba, kungiyar a jihar Neja akwai shirye shiryen da take yi yanzu na horar da manoma sanin dubarun noma, bayan nan akwai shirin baiwa mata tallafin kiwon awakai wanda za a rika barbararsu ta hanyar kimiyya, wanda shi ma za mu gabatar da shi nan bada jimawa ba.

A bayaninsa, mai martaba sarkin minna, Dakta Umar Faruq Bahago da ya samu wakilcin Cikasoron Minna, Alhaji Sulaiman Yahaya Babangida, ya jawo hankalin masu hannun da shuni da sauran kamfanonin da ke kula da harkokin  noma da su dauki irin wannan salon na karfafa guiwar kananan manoma ta yadda harkar noma zai kara tagomashi.

Mai martaba, yace yunkurin wannan kungiyar abin a yaba ne da ya kamata gwamnatoci su goyi bayan su. Haka kuma ya jawo hankalin manoma da su tabbatar sun hada kai da wannan kungiyar kuma su tabbatar sun cika alkawali dan ganin shekara mai zuwa sun kara samun gajiya fiye da na wannan shekarar.

Shugaban kungiyar ta kasa, Alhaji Sani Aliyu da ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Sale Adamu Ningi, yace wannan kungiyar hadaka ce da kungiyar AFAN, domin ita AFAN itace uwar kungiyar manoma ta kasa.

Ya cigaba da cewar kungiyar AGAFPAMA tana da rassa ga dukkanin jahohi talatin da shida har da Abuja, amma jihar Neja itace ta farko da ta fara wannan yunkurin.

Alhaji Sani Aliyu, ya jawo hankalin gwamnatin jihar Neja musamman ma'aikatar kula da harkokin noma da sauran hukumomin da abin ya shafa da su hada kai rashen kungiyar ta jihar Neja dan samun cigaba da yunkurin gwamnatin jihar na bunkasa bangaren noma.

Da yake zantawa da manema labarai, hakimin Bosso, Alhaji Mu'azu Adamu Laka, ya jawo hankalin wadanda suka samu wannan tallafin da su sani cewar wannan rance ne kuma su tabbatar zasu biya sauran kudin da ke kan su.

Hakimin ya bada tabbacin zai umurci sauran sarakunan da ke karkashin masarautarsa da su tabbatar sun sanya idanu duk manomin da ya samu wannan tallafin ya cika alkawalin da ya dauka domin wannan kayan ba na gwamnati ba ne kuma ba na siyasa ba ne rance ne dan karfafa guiwar manoma.
Kungiyar ta gabatar da sabon injimin shukar citta, dan dawo da martabar nomar citta a jihar, kasancewar jihar Neja na daga cikin jahohin da ke samar da citta a kasar nan.

No comments