Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ambaliya A Mokwa: Shaikh Zakzaky Ya Mika Da Sakon Ta’aziyya Da Jaje

Daga Zainab Rauf, Abuja Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, ya bayyana alhini da jimami kan mummunar ambaliya da...



Daga Zainab Rauf, Abuja

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, ya bayyana alhini da jimami kan mummunar ambaliya da ta afkawa garin Mokwa a jihar Neja, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da kuma raba da dama da matsugunansu.

Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar ta’aziyya da ofishinsa ya fitar a ranar Litinin, 2 ga watan Yunin 2025, inda ya yi addu’o’i ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata da kuma dawo da kwanciyar hankali ga duk wadanda lamarin ya shafa.

“sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ya afku a ƙaramar hukumar Mokwa ta jihar Neja, wanda ya yi sanadiyyar rashin rayuka, jikkata jama’a tare da hasarar dukiyoyi da dama, Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky na jajanta ma iyalan dukkan waɗanda wannan ibtila’in ya shafa”, in ji sanarwar.

“muna addu’ar Allah maɗaukakin Sarki ya jiƙan waɗanda suka rasu, da samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata; Allah kuma ya maida sabon arziki ga waɗanda suka yi hasarar dukiya. Allah Ta'ala ya kiyaye aukuwar irin wannan a nan gaba”, sanarwar ta jaddada.

Shehin Malamin ya kuma yi addu’ar samun sauki cikin gaggawa ga waɗanda suka jikkata, tare da roƙon Allah Maɗaukaki ya kare al’umma daga irin wannan masifa a nan gaba.

Ambaliyar wacce ta auku, ta yi sanadin mummunar barna, tare da jefa al’umma cikin damuwa da tausayawa a fadin ƙasar, a yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kai agaji ga waɗanda abin ya shafa.

Sakon ta’aziyyar ya fito ne ta dandalin ofishin Shehin Malamin @Szakzakyoffice, tare da alamar ƙarfafa zumunci da tausayi kamar haka: #MokwaFlood, #FreePalestine, #PrayForPalestine, da kuma #OurMartyrsOurHeroes.

 

No comments